in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a sabunta kudurin yaki da cutar kanjamau
2017-12-02 14:32:33 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a sabunta kudurin yaki da cutar kanjamau ta yadda zai zama tarihi.

A sakon da ya bayar domin ranar yaki da cutar kanjamu ta duniya, Antonio Guterres ya ce duniya na kan hanyar kawar da cutar kanjamau ya zuwa shekarar 2030. Sai dai kuma, an bar wasu sassan duniyar a baya.

Antonio Guterres ya ce mutane kusan miliyan 21 ne ke dauke da cutar kuma suke karbar magani a yanzu haka, adadin da ya kamata ya karu zuwa sama da miliyan 30 ya zuwa shekarar 2020.

Ya kara da cewa, mutuwa a sanadiyyar cutar da sabbin wadanda ke kamuwa da cutar na raguwa. Ya na mai fatan kasashen duniya za su iya cika alkawuran da suka dauka.

Sai dai Sakatare Janar din ya jadadda cewa, har yanzu da sauran rina a kaba, ya na mai takaicin yadda aka bar wasu sassan duniya a baya, da yadda a wasu yankunan, ake samun koma bayar nasarar da aka cimma da wuya, ta hanyar samun karuwar adadin mace mace sanadiyyar cutar da sabbin wadanda ke kamuwa da ita.

Mata da 'yan mata ne ke ci gaba da yawan kamuwa da cutar, musamman a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China