in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya halarci babban taron tattaunawa na jam'iyyar kwaminis ta Sin da sauran jam'iyyun siyasa na duniya
2017-12-02 13:37:36 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci bikin kaddamar da babban taron tattaunawa na jam'iyyar kwaminis ta Sin da sauran jam'iyyun siyasa na duniya jiya Juma'a a nan birnin Beijing, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai taken 'kara raya makomar duniya cikin hadin-gwiwa'.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen raya duniya mai cike da kwanciyar hankali.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya ce, ya kamata jama'a daga kasashe daban-daban su kara fahimtar juna da kawar da bambance-bambance dake tsakaninsu, a wani kokari na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Xi ya ce:

"A shekara ta 2013, karon farko na bullo da shawarar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Yanzu ina farin-cikin ganin cewa, zumunci da hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya na dada inganta, kuma wannan shawarar tawa, na kara samun goyon-baya da karbuwa daga al'ummomin duniya. Dalilin da ya sa na bada shawarar 'ziri daya da hanya daya' shi ne, tabbatar da manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. A cikin shekaru hudun da suka gabata, aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' ya zama wani babban dandali ga kasashe daban-daban don neman ci gaba tare. Na yi imanin cewa, muddin kasashe daban-daban su zama tsintsiya madaurinki daya, kwalliya za ta biya kudin sabulu."

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi jam'iyyun siyasar kasashe daban-daban su kara samun fahimtar juna da inganta ayyukan cude-ni-in-cude-ka, a wani kokari na kafa wata sabuwar dangantakar jam'iyyun siyasa tsakanin kasashe daban-daban. Shugaba Xi cewa ya yi:

"Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jam'iyya ce dake rajin kawo alheri ga al'ummar kasar. Duk abun da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi, na da nufin farfado da al'ummar Sinawa da kuma tabbatar da zaman lafiya da neman ci gaba a duniya baki daya. Ya kamata kasar Sin ta gudanar da harkokinta yadda ya kamata, abun da zai bada gudummawa ga manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Har wa yau, yayin da kasar Sin ke samun ci gaba, ya kamata ta kara samar da damammaki ga duk duniya baki daya. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba za ta shigo da wasu bakin tsare-tsare na samun ci gaban kasa ba, haka kuma ba za ta fitar da nata tsare-tsare ko kuma ta tilastawa wata kasa ta kwaikwayi nata tsarin ba. Kasar Sin za ta yi tsayin daka wajen bada gudummawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya, da neman ci gaba tsakanin kasashe daban-daban."

Shugaba Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, cikin nan da shekaru biyar dake tafe, jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta baiwa mutane 15000 na jam'iyyun siyasar kasashen duniya damar zuwa nan kasar Sin domin yin mu'amala. Xi ya kuma bada shawarar kafa babban tsari na gudanar da taron tattaunawa tsakanin jam'iyyar kwaminis ta Sin da jam'iyyun siyasar kasashe daban-daban.

Bayan bikin kaddamar da babban taron tattaunawa na jam'iyyar kwaminis ta Sin da sauran jam'iyyun siyasa na duniya a birnin Beijing, an gudanar da cikakken zaman taro na farko, inda wasu shugabannin jam'iyyun siyasa na duniya suka gabatar da jawabi daya bayan daya, ciki har da shugaban jam'iyyar People's Party, kana firaministan kasar Kambodiya, Hun Sen, da shugabar gwamnatin kasar Myanmar, Madam Aung San Suu Kyi, da kuma mataimakin shugaban jam'iyya mai mulki a kasar Habasha, wato jam'iyyar EPRDF, kana mataimakin firaministan kasar, Demeke Mekonnen. A cikin jawabansu, wadannan manyan jami'ai sun yabo kwarai da shawarar da shugaba Xi Jinping ya bayar, wato gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da raya kyakkyawar duniya cikin hadin-gwiwa, haka kuma sun nuna cewa, za su kara yin kokari tare da jam'iyyar kwaminis ta Sin, domin raya wata duniya mai kyakkyawar makoma.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban jam'iyya mai mulki a kasar Habasha, wato jam'iyyar EPRDF, kana mataimakin firaministan kasar, Demeke Mekonnen ya bayyana ra'ayinsa, inda ya ce kasar Sin ta dade tana fadakar da jam'iyyun siyasar kasashen Afirka daban-daban kan nasarorin da ta samu a fannin raya kasa, abun da ya aza tubali mai inganci ga manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma.

Shi ma a nasa bangaren, babban sakataren jam'iyyar Rassemblement Populaire pour le Progres mai mulki a kasar Djibouti ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dukufa ka'in da na'in wajen gina wata dangantakar hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka cikin daidaito, kana, irin wannan kyakkyawar alaka dake tsakanin jam'iyyun siyasar Sin da Afirka, ba hakaba dangantakar Sin da kasashen Afirka kadai za ta yi ba, har ma da karfafa dankon zumunci tsakanin al'ummomin kasashen duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China