in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar yaki da cutar AIDS ta duniya
2017-11-30 09:22:36 cri
Ana bikin wannan rana ce a ranar 1 ga watan Disamban kowace shekara domin ilimantar da jama'a game da cutar, illolinta,abubuwan dake haddasa yaduwarta, matakan kariya da sauransu.

Bugu da kari, wannan rana, wata dama ce ga jama'a a duniya baki daya su hada kai a kokarin da ake yi na yaki da cutar, nuna wa masu dauke da cutar goyon baya, tare da tunawa da wadanda suka kwanta dama sanadiyar cutar.

Wannan rana, ita ce rana ta farko a duniya da ta shafi harkokin kiwon lafiya kuma an fara bikin ranar ce a shekarar 1988.

Bayanai na nuna cewa, akwai mutane sama da miliyan 30 da ke dauke da cutar a duniya, inda sama da mutane miliyan 20 suka mutu tsakanin shekarar 1981 da shekarar 2007 sanadiyar kwayar cutar. Kana a shekarar 2016, kaso 76 cikin 100 na mata masu juna biyu dake dauke da kwayar cutar a duniya ne suke karbar maganin hana yada cutar ga jaririn da suke dauke da shi. Baya ga sama da mutane miliyan 19 dake karbar maganin rage kaifin cutar.

Tun lokacin da aka bullo da shirin yaki da cutar Sida na majalisar dinkin duniya (UNAIDS) a shekarar 2004, shirin ya himmatu wajen ilimantar da jama'a tare da zabar take ko jigon da zai kasance a ranar yaki da cutar ta kowace shekara ta hanyar tattaunawa da sauran kungiyoyin lafiya na duniya.

Masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar yaki da cutar ta kanjamau, wajibi ne a samar da magungunan rage karfin cutar ga masu fama da ita, magance tsangwama da wariyar da ake nuna musu, sannan jama'a su tsaya ga iyalansu da daukar matakan da masana kiwon lafiya suka zayyana don kariya daga kamuwa da wannan cuta mai hallaka jama'a. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China