Yau Laraba, mataimakin sakataren ofishin kula da harkokin Afirka ta jam'iyyar NCP dake kasar Sudan, Saifeelislam Omer Elimam, wanda a yanzu haka yake halartar taron karawa juna sani tsakanin jam'iyyun siyasun Sin da Afirka karo na uku a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, jam'iyyarsa na matukar son inganta alaka da jam'iyyar kwaminis ta Sin, a wani mataki na neman ci gaba tare.
Yayin da yake zantawa da wakiliyar CRI a yau, Saifeelislam Omer ya godewa jam'iyyar kwaminis ta Sin saboda goyon-bayan da ta dade take nuna mata, kana, jam'iyyar NCP ta Sudan na fatan yin amfani da wannan dama, domin kara koyon nasarorin da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta samu a fannin tafiyar da mulkin kasa.(Murtala Zhang)