in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattaunawa da gwamnan jihar Taraba Mr. Darius Dickson Ishaku (A)
2018-01-24 16:20:47 cri
A kwanakin baya ne aka bude taron baje kolin kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa, da wadanda ake bukata domin bunkasa ayyukan masana'antu na kasashen ketare, karo na 9 wanda kasar Sin ke shiryawa.

Taron na yini biyu ya gudana ne a nan birnin Beijing, ya kuma samu mahalarta baki, da wakilan gwamnatoci da hukumomi da 'yan kasuwa daga kasashen duniya da dama.

Cikin mahalartan dai akwai tawagar gwamnatin jihar Taraba dake tarayyar Najeriya, karkashin jagorancin gwamnan jihar Mr. Darius Dickson Ishaku.

Abokin aikin mu Saminu Alhassan, ya zanta da gwamnan na jihar Taraba, game da tasirin wannan taro, da kuma irin alfanun sa ga al'ummar da yake wakilta, da ma irin tasirin dake akwai game da dangantakar kasar Sin da tarayyar Najeriya.


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China