A wannan mako, shirin Sin da Afirka ya ziyarci birnin Tianjin na kasar Sin, inda abokin aikinmu Murtala Zhang ya halarci wani taro karawa juna sani tsakanin Sin da Afirka game da musayar ilimi da hadin-gwiwar raya masana'antu, a wajen taron ya samu zantawa da Malam Gambo Babandi Gumel, na sashen nazarin tattalin arziki a jami'ar tarayyar ta Dutse, a jahar Jigawa dake tarayyar Najeriya, inda ya gabatar da wani jawabi mai taken "Kalubaloli da hasashe ta fuskar masana'atu da kuma cigaban ilmi a Afrika: Darrusa da nahiyar Afrika zata koya daga kasar Sin". A cikin tattaunawar da Murtala Zhang yayi da masanin tattalin arzikin, ya yi fashin baki dangane da irin darrusan da kasashen Afrika za su koya da kuma irin dabarun da kasar ta yi amfani da su wajen habaka ci gaban tattalin arziki da masana'antunta har ta kai matsayin da ta tsinci kanta a halin yanzu.
171212-Tattaunawa-da-shehun-malami-Gambo-Babandi-Gumel-daga-jamiar-gwamnatin-tarayya-dake-birnin-Dutsen-jihar-Jigawar-Najeriya.m4a
|