A wannan mako, shirin Sin da Afirka ya ziyarci birnin Tianjin na kasar Sin inda abokinmu Murtala Zhang ya halarci wani taro karawa juna sani tsakanin Sin da Afirka game da musayar ilimi da hadin-gwiwar raya masana'antu, a wajen taron ya samu zantawa da Kabiru Adamu Kiyawa wani masanin tattalin arziki wanda ke aiki a jahar Jigawa dake tarayyar Najeriya inda ya gabatar da wani jawabi mai taken matsayin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika ta fuskar masana'antu a halin yanzu: Nasarori da kalubaloli.
A cikin tattaunawar da Murtala Zhang yayi da shi wannan masanin, ya bayyana ra'ayinsa dangane da hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannonin masana'antu da cinikayya da darussan da ya kamata Afirka ta koya daga kasar Sin.
171205-Tattaunawa-da-Kabiru-Adamu-Kiyawa-wanda-shi-ne-masanin-tattalin-arziki-daga-jihar-Jigawar-tarayyar-Najeriya.m4a
|