in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan ruwan Argentina ta ce an ji wata kara a yankin da ake neman jirgin karkashin ruwan kasar da ya bace
2017-11-24 10:18:01 cri
Rudunar sojojin ruwan kasar Argentina ta tabbatar a jiya Alhamis cewa, an ji wata kara a yankin da ake aikin neman jirgin karkashin ruwan kasar da ya bace tun ranar 15 ga wannan wata dauke da mutane 44 a cikinsa.

Mai Magana da yawun rundar sojojin ruwan kasar Enrique Balbi ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Amurka da hukumar kula da gwajin nukiliya dake Austria ne suka tabbatar da wannan labari.

Balbi ya ce suna ci gaba da aikin neman jirgin karkashin ruwan, amma har yanzu babu tabbaci ko za a ci gaba da aikin neman sa.

A ranar Litinin ne dai aka shirya jirgin karkashin ruwa na kasar ta Argentina mai suna San Yuan da ya bace a yankin kudancin tekun atilantika zai isa sansanin sojojin ruwa dake Mar del Plata, kimanin kilomita 250 kudu maso gabashin Boenos Aires.

An daina jin duriyar jirgin ne a lojacin da yake yankin ruwan San Jorge, kimanin kilomita 432 kudu maso gabashin zirin Valdes a kudancin tekun Atilantika. An kuma daina jin duriyarsa kwata-kwata da misalin karfe 7.30 na safiyar ranar 15 ga watan Nuwamba agogon Argentina, har zuwa wannan lokaci.

Balbi ya karyata rade-raden da ake yi cewa, an kaiwa jirgin karkashin ruwan hari ne, yana mai cewa, Babu wata shaida dake tabbatar da hakan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China