in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta mayar da yankin Xiongan mai dausayin ciyayi
2017-11-24 09:39:35 cri
Kasar Sin ta kammala tsara wani jadawali kare muhalli ga yankin Xiongan dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin, da nufin mai da shi dausayin ciyayi na zamani.

Yayin wani taron manema labarai, shugaban cibiyar binciken tsare-tsaren kare muhalli ta kasar Sin Wang Jinnan, ya ce jadawalin zai dace da muradun kare Baiyangdian, tafki mafi girma dake arewacin kasar kuma guri mai muhimmanci a yankin Xiongan.

Bisa matakan kare muhallin hallitu da inganta muhalli tare da ba batun raya tsirrai muhimmanci, Xiongan zai zama yanki mai karancin sinadarin Carbon, da kyan yanayin rayuwa, kana birni mai muhimmanci a duniya da mutane da sauran hallitu za su rayu cikin kwanciyar hankali.

Wani Jami'in ma'aikatar kare muhalli ta kasar Sin You Yanxin, ya ce Gwamnatin tsakiyar kasar ta ware yuan miliyan 500 kwatankwacin dala biliyan 76 domin inganta muhallin yankin.

A watan Afrilun da ya gabata ne kasar Sin ta yanke shawarar kafa sabon yankin Xiongan, sabon yanki na uku dake da muhimmanci ga kasar bayan yankin musammam na raya tattalin arziki na Shenzhen da sabon yankin Shanghai Pudong. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China