Hoh Xil ma'anarsa a cikin harshen Mongoliya shi ne shudin tsauni, sa'an nan, yana kuma da nufin budurwa mai kyau a cikin harshen Xizang wato na al'ummar Tibet. Kasancewarsa a tudun Plateau na Qinghai-Tibet, ana fuskantar matsanancin dari, da karancin iskar shaka a yankin Hoh Xil, don haka da wuya dan Adam ya dade yana rayuwa a wurin. Duk da haka, ubangiji ya halicci nau'o'in halittu na musamman da suke iya jure irin wannan yanayi na yankin, ciki har da nau'in gada da ake kira gadar Tibet, gadar da ake daukaka ta a matsayin abin alfahari na Hoh Xil.Sai dai a karshen karni na 20, sakamakon yadda wani nau'in mayafin da ake kira Shahtoosh, wanda ake sakawa da gashin gadar yake matukar samun karbuwa a kasuwannin kasashen yammci, nau'in gadar sun taba kasancewa daf da karewa daga doron kasa. A kasance tare da mu domin jin karin haske.(Lubabatu)
171117-suonan-da-mabiyansa-lubabatu.m4a
|