Wasikar murabus din ta ruwaito shugaba Mugabe na cewa, 'Ni Robert Gabriel Mugabe, bisa sashe na 96 karamin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin Zimbabwe, ina mika murabus dina a hukumance a matsayin shugaban kasar Zimbabwe nan take'
Murabus din na zuwa ne kwanaki 2 bayan jam'iyyar Zanu PF mai mulkin kasar ta cire Mugabe a matsayin shugabanta tana mai kiran ya sauka daga mulkin kasar bisa jerin wasu tuhume-tuhume
Jam'iyyar ta nemi Mugabe ya yi murabus kafin karfe 12 na ranar Litinin, sai dai ya yi watsi da wa'adin, al'amarin da ya sa 'ya'yan majalisar dake majalisun dokoki su fara yunkurin tsige shi a jiya.
Sai dai, bayan fara yunkurin sai kawai Mugabe ya yi murabus, al'amarin da ya kawo karshen mulkin kusan shekaru 40 yana yi a Zimbabwe.(Fa'iza Mustapha)