in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nan ba da dadewa ba ake saran mataimakin shugaban kasar Zimbabwe da aka kora zai dawo gida
2017-11-21 11:54:29 cri
Babban hafsan sojojin kasa na Zimbabwe Constantino Chiwenga ya shaidawa taron manema labarai jiya Litinin cewa, sun gamsu da tattaunawar da za a yi tsakanin shugaba Robert Mugabe da tsohon mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, wanda ake saran zai dawo kasar nan ba da dadewa ba, bayan ya fice daga cikin kasar makonni biyun da suka gabata. Za kuma a sanar da 'yan kasar sakamakon wannan tattaunawa.

Ya ce, a halin yanzu shugaba Mugabe wanda jam'iyyarsa ta Zanu-PF ta tsige shi daga shugabancinta a ranar Lahadi, ya fara tsara matakan magance wannan dambarwa da ma taswirar makomar kasar.

Chiwenga ya ce,yayin da hakan ke gudana, suna kira ga 'yan kasar ta Zimbabwe da su zauna cikin lumana, kana su kasance masu martaba dokokin kasa. Yana mai cewa, tattaunawar da sojojin kasar suka yi da Mugabe ta gudana cikin yanayi na mutunta juna kuma an cimma tudun dafawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China