171122-Taron-Apec-na-shekarar-2017.m4a
|
Taron na bana, shi ne na biyu da aka gudanar a kasar Vietnam, bayan wanda aka shirya a shekarar 2006. Wannan shi ne taro na farko da shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Kudu da jagorar yankin Hong Kong na kasar Sin da Firaministan New Zealand suka halarta tun bayan rantsar da su a kan mukamansu.
Manufar taron kungiyar wadda aka kafa a shekarar 1989, ita ce bunkasa harkokin cinikayya ba tare da wani shamaki ba a yankin. Haka kuma taron na bana ya amince a kara yin mu'amula da juna a wannan yanki tare da mayar da yankin a matsayin muhimmin yankin hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, karfafa yankin cinikayya cikin 'yanci, samar da ci gaba mai dorewa ba tare da la'akari da wani bambance-bambance ba.
Sauran sun hada da taimakawa hukumomin cinikayya da kanana da matsakaitan masana'antu, samar da abinci da kuma uwa uba raya aikin gona.
Masana na cewa, taron wani dandali ne dake karfafa martaba dokokin cinikayya da yin takara da nuna daidaito tsakanin kasashe. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)