Hukumar ta ce ta kira wani zaman taro na hoton bidiyo, inda ta kara fahimtar halin da ake ciki a wurin da bala'in ya auku, tare kuma da kiran kwararru daga hukumomin kula da harkokin girgizar kasa na lardunan Yunnan da Sichuan, don su taimakawa Xizang nazarin girgizar da ta auku a wannan karo, gami da wanda ka iya faruwa a nan gaba.
Su ma a nasu bangaren, wasu kwararru daga hukumar kula da harkokin girgizar kasa ta kasar Sin, wadanda a yanzu haka suke gudanar da ayyuka a yankin Xizang, sun garzaya zuwa yankin da biftila'in ya shafa, a wani kokari na taimakawa mahukuntan yankin gudanar da ayyukan shawo kansa. (Murtala Zhang)