in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmacin alakar Sin da Amurka ga wanzuwar zaman lafiya a duniya
2017-11-16 16:02:07 cri

Daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Nuwanban shekarar 2017 ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kawo ziyarar aiki ta kwanaki uku a nan kasar Sin, ziyarar da ta janyo hankulan kasashen duniya matuka.

Ziyarar shugaba Trump a kasar Sin ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar ta Sin tun bayan da ya zama shugaban kasar Amurka, kana ziyara ta farko da wani shugaban kasa ya kawo kasar Sin, tun bayan kammala babban taron wakilan JKS karo na 19, taron da ya kai ga sake zaben Xi Jiping a matsayin babban sakataren JKS, kana shugaban rundunar askarawar kasar.

Wannan ziyara tana da muhimmanci ga kasashen biyu, kasancewar kasar Sin babbar kasa mai tasowa a duniya, yayin da ita kuma Amurka ta kasance babbar kasa mafi ci gaba a duniya. Kana manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya. Yayin ziyarar, kasashen biyu sun kulla yarjejeniyoyin cinikayya da darajarsu ta kai sama da dala biliyan 200 a fannonin makamashi, kirkire-kirkire da harkokin masana'antu, da aikin gona da batun sararin samaniya da sauransu.

Mahukuntan kasar Sin sun suke jaddada cewa, manufar kasar game da bude kofa ga kasashen ketare ba za ta canja ba. Haka kuma za ta kyautata wannan manufa ta yadda za a samar da yanayin da ya dace ga kamfanonin ketare ciki har da na kasar Amurka.

Bugu da kari, shugaba Xi, ya nanata matsayin kasarsa game da batun zirin Koriya na komawa ga teburin sulhu da martaba kudurorin kwamitin sulhu na MDD, don warware wannan takaddama cikin ruwan sanyi.

Masu fashin baki na cewa, ziyarar za ta taimaka wajen rage zaman tankiya da bahaguwar fahimta tsakanin sassan biyu kan wasu muhimman batutuwa kamar, satar bayanan intanet, kare hakkin bil-Adam, tsaron nukiliya da makamantansu. Inda ake fatan karkaka ga batun cinikayya, amincewa da mutunta juna da sauran matakan inganta rayuwar bil-adam da uwa uba samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China