in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar yaki da cin zarafin 'yan jarida ta duniya
2017-11-16 16:00:58 cri
Ranar 2 ga watan Nuwanban kowa ce shekara, rana ce da MDD ta kebe da nufin Ilimantar da jama'a game da cin zarafin 'yan jarida da ma'aikatan kafofin watsa labarai a sassa daban-daban na duniya.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2017 da muke ciki kadai, an halaka 'yan jarida sama da Talatin, kana sha daya(11) daga cikin wannan adadi, an yi musu kisan gilla ne. Sannan kuma a shekarar 2016 dacta gabata, an kashe 'yan jarida kimanin arba'in da takwas(48), 16 daga cikin wannan adadin an yi musu kisan gilla ne. Galibin lamarin na faruwa ne a kasashen da ake keta hakkin bil-Adam, yayin da 'yan jaridar ke kokarin bankado wasu rahotanni ko muhimman bayanai domin sanar da jama'a abubuwan dake faruwa, wadanda a mafi yawan lokuta ba sa yiwa mahukunta dadi.

Koda yake masu fashin baki na cewa, wasu lokutan kuma su ma 'yan jaridar na karya ka'idojin aikinsu yayin tattara irin wadannan bayanai, lamarin dake kaiwa ga kame, musgunawa a wasu lokutan kuma har ta kai ga asarar rayuka.

Daga shekarar 2006 zuwa 2016, sama da 'yan jarida 900 ne suka gamu da ajalinsu yayin dauko rahotanni. Hukumar UNESCO ta nuna damuwa matuka kan wannan lamari, tana mai kira da a gaggauta gurfanar da masu cin zarafin 'yan jarida a gaban kuliya da nufin hukunta su.

Haka kuma, an bukaci kungiyoyin 'yan jarida da su rika tantance 'yan jarida na gaskiya da na karya, kana a karfafawa 'yan jarida na hakika gwiwar martaba ka'idojin aikin. A hannu guda kuma, mahukunta su rika daukar 'yan jarida a matsayin abokai maimakon abokan gaba, domin 'yan jarida suna aikin ne a matsayin masu sanar da jama'a abin da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China