in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na taro game da kyandar birai
2017-11-07 20:24:10 cri
Kwararru a fannin kiwon lafiya daga hukumar lafiya ta duniya WHO, da takwarorinsu na kasashen Uganda, da Kenya, na taro a gundumar Kapchorwa dake gabashin kasar Uganda, domin tattauna batutuwa masu alaka da shawo kan cutar kyandar birai mai matukar hadari ga bil adama.

Kwararrun dai na fatan yin musayar kwarewa, game da dabarun kandagarki da dakile yaduwar cutar a kan iyakokin kasashen makwaftan juna.

Yanzu haka dai an tattara alkaluman mutane 6 da suka kamu da cutar, cikin hadda uku da tuni suka rasu, da biyu da aka tabbatar suna dauke da ita, sai kuma mutum guda da ake ganin mai yiwuwa yana dauke da cutar, baya ga wasu mutum uku da ake sa ido kan su domin hakikance ko sun kamu da cutar, tun bayan bullar ta a cikin watan da ya gabata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China