in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta harba wasu taurarin dan Adam na Beidou
2017-11-06 10:49:10 cri

A jiya Lahadi, wato 5 ga watan Nuwamba, kasar Sin ta yi amfani da roka samfurin lamba 3 na Changzheng wajen harba taurarin dan Adam biyu dake jagoranci ga harkokin zirga-zirga. Wannan nasara ta sa kasar Sin ta shiga sabon mataki na kafa sabon tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou da zai shafi fadin duniya baki daya.

Da misalin karfe 8 saura kwata na jiya da dare, wata roka samfurin Changzheng mai lamba 3 dauke da taurarin dan Adam biyu na ba da jagoranci ga zirga-zirga ta tashi daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Xichang ta kasar Sin zuwa sararin samaniya. Wadannan taurarin dan Adam su ne na 24 da na 25 a tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou, wannan ne kuma karo na farko da kasar Sin ta harba taurarin dan Adam game da sabon tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou. Bayan sa'o'i hudu na shigar wadannan taurarin dan Adam biyu can sararin samaniya, fikafikan baturansu suka bude kamar yadda aka tsara. Sabo da haka, Mr. Zhang Xueyu, direktan cibiyar harba taurarin dan Adam ta Xichang ya shelanta cewa, an samu nasarar harba taurarin dan Adam na sabon tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou. "Yanzu na shelanta cewa, mun samu nasarar harba taurarin dan Adam gaba daya."

Rahotanni na cewa, bayan da kasar Sin ta samu nasarar harba wadannan taurarin dan Adam na sabon tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou a karo na farko, za a kara saurin sanya sabon tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou ta yadda zai rika ba da hidima a duk fadin duniya. Manjo-janar Yang Changfeng, babban mai fasalta tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou ya bayyana cewa, "Nasarar harba sabon tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou na wannan karo, ta alamta cewa, mun shiga sabon zamani na kafa sabon tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou a duk fadin duniya. Sakamakon haka, za mu iya yada ilmi da fasahar yin amfani da wannan tsari na Beidou da kuma bunkasa shi kamar yadda ake bunkasa wata sana'a a duk fadin duniya. Kasar Sin da sauran kasashen duniya za su iya kara yin hadin gwiwa wajen yin amfani da wannan tsari na Beidou."

Tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou wani muhimmin al'amari a harkokin yau da kullum na sararin samaniya ga kasar Sin. A shekarar 2009 ne, kasar Sin ta kaddamar da aikin kafa wannan sabon tsari na Beidou. A cikin shekaru 8 da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaba kan wasu muhimman fasahohi, inda ta yi nasarar kammala gwaje-gwajen sabbin taurarin dan Adam na zamani. Musamman a shekarar 2015 da kuma 2016, Kasar Sin ta samu nasarar harba sabbin taurarin dan Adam masu ba da jagoranci ga zirga-zirga na zamani guda 5, har ma ta kammala gwada su a lokacin da suke zirga-zirga a kan hanyoyinsu na zuwa sararin samaniya.

Bisa shirin da aka tsara, kasar Sin za ta kara harba wasu taurarin dan Adam masu ba da jagoranci ga harkokin zirga-zirga. Ya zuwa shekarar 2018, za ta harba irin wadannan taurarin dan-Adam 18 domin kafa sabon tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou. Sannan ya zuwa shekarar 2020, za ta kammala aikin harba dukkan taurarin dan Adam na ba da jagoranci ga zirga-zirga guda 30 domin kammala aikin kafa wannan sabon tsarin zirga-zirga na taurarin dan Adam na Beidou. Sakamakon haka, wannan tsari zai iya ba da hidima a duk fadin duniya baki daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China