Daraktan sashen yaki da hana yaduwar haramtattun makamai a ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mikhail Ulyanov, ya bayyana cewa, sun tsawaita wa'adin gudanar da binciken, a cewarsa batun amfani da makamai masu guba lamari ne da ba za'a amince dashi ba, kuma yana fatan abokan huldarsu na MDD zasu amince da gudanar da binciken.
Sai dai ya fada a taron manema labarai cewa, hukumar dake haramta amfani da makamai masu guba (OPCW) tare da hadin gwiwar sashen bincike na MDD (JIM), sun kaddamar da shirin bincike kan amfani da makamai masu guba a Syria, amma a cewarsa, kamata ya yi su fara aiki na gaske, ba kamar yadda suke yi yanzu.
Ulyanov ya ce, daga bisani a ranar Alhamis kasar Rashar zata gabatar da nata kudurin ga kwamitin tsaron MDD game da batun tsawaita wa'adin binciken wanda aka damka alhakinsa ga JIM, wanda ya samu amincewar sakatare janar na MDD da shugaban OPCW.