in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta farauto 'yan kasar 3,317 da suke neman mafaka a kasashen ketare
2017-11-03 10:24:13 cri
Ma'aikatar tsaron al'umma ta kasar Sin ta sanar da cewa, jami'an 'yan sandan kasar sun yi nasarar tusa keyar Sinawa 3,317 wadanda ke neman mafaka a kasashe da shiyyoyin duniya sama da 120 cikin shekaru 5 da suka gabata.

Karkashin shirin Fox Hunt, wanda ke neman 'yan kasar ta Sin da suka tsere kasashen waje domin gujewa amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu na zarginsu da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi tattalin arziki.

Sakamakon yin hadin gwiwa da wasu hukumoni da kuma yin amfani da sabbin fasahohin zamani hakan ya taimakawa shirin wajen gano 'yan kasar da suka yi badda kama ko kuma ta hanyar sauya fuskokinsu, inji ma'aikatar.

A cikin shekarun biyar da suka gabata, kasashen Greece, Bulgaria, Italy da kuma sauran kasashe da shiyyoyi, sun tusa keyar Sinawa 16 da ake zarginsu da aikita laifuka sakamakon bukatar da gwamnatin Sin ta gabatar musu, bugu da kari, wasu Sinawan 17 da ake zargi sun dawo kasar Sin a bisa radin kansu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China