in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani dan kasuwa zai shigar da karar Guo Wengui a gaban kotu
2017-11-02 10:05:26 cri
Wani dan kasuwa Qu Long, ya bayyanawa manema labarai a jiya cewa, zai shigar da karar Dan kasuwar nan Guo Wengui, da ya kulla masa makarkashiyar da ta yi sanadiyyar kai shi gidan yari.

Qu Long, ya ce Guo Wengui ya kulla masa sharri ne saboda ya tona asirin sama da fadi da dukiyoyin kasa da ya yi, yana mai cewa Guo ya aikata munanan laifuffuka.

Qu Long ya kuma yi kira ga kasar Amurka, da ta maido da Guo kasar Sin, wanda a yanzu haka yake gudun hijira a can.

Yayin da yake ganawa da manema labarai, Qu Long ya bayyana ta yadda ya fara sanin Guo Wengui da yadda suka kulla alaka da kuma dalilin da ya sanya Guo ya kulla masa sharrin da ya kai shi gidan wakafi.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Qu Long ya ce, bayan wanke shi daga laifin da ake zarginsa da aikatawa, shi da lauyansa na kokarin tattara bayanai dangane da wannan shari'a, kuma za su shigar da karar Guo Wengui a gaban kuliya, don a yanke masa hukunci tare da cigiyar dukiyoyin da ya sace. Har wa yau, Qu Long da lauyansa za su gabatar da takardu ga hukumomin shari'a na kasar Amurka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China