171101-Tasirin-babban-taron-JKS-karo-na-19-ga-ci-gaban-kasashen-duniya.m4a
|
An kawo karshen taron ne bayan da aka zabi sabbin mambobi kwamitin koli da na kwamitin ladaftarwa na jam'iyyar. A hannu guda kuma wakilai mahalatar taron, sun zartas da kuduri game da rahoton da kwamitin koli na taron jam'iyyar karo na 18 ya gabatar. An kuma amince da gyaran fuskar da aka yiwa kundin tsarin mulkin JKS, wanda aka sanya tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki a matsayin jigon tafiyar da muradun JKS bisa salo na musamman na gurguzu mafi dacewa da kasar Sin.
Bayan wannan taro shugabannin kasashe da jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kasa da kasa da dama sun aiko da sakonnin fatan alheri da taya murna game da kammalar taron cikin nasara, da ma bayyana irin nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin shekaru biyar din da suka gabata karkashin JKS wadda shugaba Xi Jinping ke jagoranta.
Masu sharhi sun bayyana imanin cewa, manufofin raya kasa da wakilan taron suka tsara, za su kara sanyan kasar Sin bisa turbar samun wasu tarin nasarori wadanda za su amfani duniya baki daya nan da wasu shekaru biyar masu zuwa bisa jagorancin Xi Jinping. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)