in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara mai da hankali kan ingancin ci gaban tattalin arziki
2017-10-31 10:42:33 cri

Kwanakin baya ne aka gudanar da taron shekara shekara na tattalin arzikin kasar Sin da hadin gwiwar sauran kasashen duniya. Taron da ya gudana a nan birnin Beijing na da taken "Sin da kasashen duniya bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19", inda kwararru mahalarta taron suka nuna ra'ayin cewa, yanzu haka tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya shiga mataki na samun ci gaba mai inganci, a saboda haka bukatu a fannin hadin gwiwa tsakanin kasar ta Sin da sauran kasashen duniya za su kara habaka.

A cikin rahoton da aka fitar bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, an bayyana cewa, za a tsara salon tattalin arziki na zamani a kasar, kana an yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya riya ya shiga mataki na samun ci gaba mai inganci daga mataki na samun ci gaba cikin sauri, shi ya sa ya zama wajibi a tsara tsarin tattalin arziki iri na zamani domin biyan bukatun ci gaban kasar Sin bisa manyan tsare-tsare.

Shehun malamin kwalejin koyon ilmin tattalin arziki ta jami'ar Peking dake nan birnin Beijing Su Jian yana ganin cewa, babu sabanin tsakanin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci da samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri, wato ana iya cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci cikin sauri idan aka dauki matakai masu dacewa, inda ya ce, "A cikin shekaru talatin masu zuwa, wato tsakanin shekarar 2020 da ta 2050, hakika kasar Sin za ta fuskanci kalubale wajen karuwar tattalin arziki, yanzu kasar Sin tana kokarin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, amma idan an dauki matakai da suka dace, za a iyar cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci cikin sauri, duba da cewa babu sabani tsakanin inganci da sauri, idan an yi kokari matuka."

Kwararru mahalarta taron da dama suna ganin cewa, tsara tsarin tattalin arzikin zamani yana da nasaba da kasuwa da kuma sarrafawar gwamnatin kasar, saboda kasuwa za ta taka rawa wajen raba albarkatu, gwamnatin kuwa za ta iya sarrafa kasuwa ta hanyar yin kirkire kirkire bisa manyan tsare-tsare.

Shugaban zartaswa na cibiyar nazari kan aikin raya kasa kuma mataimakin shguaban jami'ar Renmin ta kasar Sin Liu Yuanchen ya dauka cewa, a sabon zamanin da ake ciki yanzu, manufar yin kwaskwarimar da kasar Sin ke aiwatarwa ta sauya, yanzu haka an hada tattalin arziki da kasuwa gu daya yayin da ake kokarin yin gyaran fuska, ya ce, "Da farko, za a gudanar da kwaskwarima kan harajin da ake biya, da batun dake shafar babbar moriyar kananan gwamntocin wurare daban daban a fadin kasar Sin. Na biyu, za a yi kwaskwarima kan tsarin sa ido a aikin hukumomin gwamnati. Na uku, za a yi gyaran fuska kan tsarin yada manufofin kasa masu nasaba da hakan. Na hudu, za a yi kokarin kyautata tunanin gargajiya a fannin tafiyar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da harkokin gwamnati; Misali, a baya an bayyana cewa, kamata ya yi a raba aikin jam'iyyar kwaminis da aikin gwamnati, amma yanzu ana tafiyar da harkokin biyu a ofishi guda cikin hadin gwiwa, wannan babban sakamako ne da aka samu."

Kana an fitar da sabuwar manufar harkokin waje ta kasar Sin a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, wato za a kafa sabuwar huldar dake tsakanin kasa da kasa, tare kuma da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama.

Shugaban kwalejin koyon ilmin huldar dake tsakanin kasa da kasa ta jami'ar Peking Jia Qingguo ya dauka cewa, nan gaban bukatun kasar Sin a fannin hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya za su habaka, ya ce, "Makasudinmu shi ne gudanar da hadin gwiwa domin samun moriya tare, yanzu haka daukacin kasashen duniya suna fuskantar matsaloli da kalubale iri daya kamar a fannin ciniki, da zuba jari, da dakile aikata laifuffuka a ketare, da yin kaura ba bisa doka ba, da ta'addanci, da matsalar muhalli, da tsaron yanar gizo, da manyan makamai na kare dangi da sauransu. Sannu a hankali, bukatun da kasar Sin take da su wajen hadin gwiwa da sauran kasashen duniya za su kara habaka."

Mahalartan taron su ma sun bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufarta ta samun ci gaba cikin lumana, tare kuma da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin manyan kasashe.

Kan huldar dake tsakanin Sin da Amurka, shehun malamin jami'ar Renmin ta kasar Sin Zhang Shengjun ya bayyana cewa, nan gaba kasashen biyu wato Sin da Amurka za su kara habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, saboda hakan zai amfanawa sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China