in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tsara yanayin tattalin arzikin zamani a kasar Sin
2017-10-30 10:59:08 cri

A ranar 28 ga wata, aka kaddamar da taron shekara shekara na tattalin arzikin kasar Sin da hadin gwiwar sauran kasashen duniya. Taron da ya gudana dake nan birnin Beijing, na da taken "Sin da kasashen duniya bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19", inda kwararru mahalarta taron na tattalin arziki suka tattauna sosai kan batun da aka tabo a cikin rahoton da aka fitar, bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis na kasar Sin karo na 19, game da tsara yanayin tattalin arziki iri na zamani a kasar Sin.  

Mahalartan taron suna ganin cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ingancin kayyayaki, yayin da ake kokarin raya tattalin arziki a kasar. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta kara ba da muhimmanci kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin kirkire kirkire.

Yayin taron da aka gudanar, mataimakin daraktan cibiyar nazari kan aikin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yiming ya bayyana cewa, bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, tattalin arzikin kasar Sin zai yi manyan sauye-sauye a fannoni biyar, inda ya ce, "Da farko, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasawa cikin sauri kamar yadda yake a halin da ake ciki yanzu, a saboda haka ya kamata a kara mai da hankali kan ingancin kayayyaki; na biyu, lokaci bayan lokaci, yanayi na gargajiya zai rika tafiyar hawainiya, ba zai yiwu ya ci gaba da samun bunkasa cikin sauri ba. Don haka sabon salon gudanarwa zai samu bunkasa lami lafiya; na uku, za a kara mai da hankali kan aikin mayar da garuruwa na zamani a yawancin lardunan dake fadin kasar; na hudu, bukatun makamashi da muhimman albarkatun ma'adinai za su karu; na biyar, nan gaba a bayyane take tattalin arzikin kasar Sin zai kara taka rawa a fannin tattalin arzikin duniya."

A cikin rahoton da aka fitar bayan babban taron wakilan JKS karo na 19, a karo na farko an gabatar da cewa, za a tsara salon tattalin arziki irin na zamani a kasar Sin, game da yadda za a cimma burin, Wang Yiming ya bayyana cewa, "A cikin rahoton, an bayyana cewa, abu mafi muhimmanci shi ne ingancin kayayyaki, kana an jaddada cewa, ya zama wajibi a kara zurfafa gyaran fuska ga tsarin samar da kayayyaki. Ban da haka kuma, kamata ya yi a tsara wani tsari na sha'anin, ta hanyar kafa kamfanonin samar da kayayyaki, da yin kirkire kirkire a fannonin kimiyya da fasaha, tare kuma da tattara kudaden da ake bukata. Kaza lika, yana da muhimmanci a tsara wani tsarin tattalin arzikin dake kumshe da tsarin kasuwa mai inganci, tare kuma da sarrafawa ta gwamnati mai karfi. Ina ganin cewa, hakan shi ne tsarin tattalin arziki irin na zamani."

Wang Yiming ya ci gaba da cewa, idan ana son tsara tsarin tattalin arziki iri na zamani a kasar Sin, kamata ya yi a kara zurfafa kwaskwarima a fannonin kyautata tsarin samar da kayayyaki, da hanzartar kafa kasa mai kirkire kirkire, da aiwatar da manufar farfado da kauyuka a kasar, da sa kaimi kan aikin bude kofa daga duk fannoni da sauransu.

Shehun malamin jami'ar Nanjing ta lardin Jiangsu na kasar Hong Yin ya yi nuni da cewa, idan ana son tsara salon tattalin arziki irin na zamani a kasar Sin, dole a kara yin kirkire kirkire domin samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya, inda ya ce, "Kamfanonin kasar Sin sun shiga kasuwar kasashen duniya, hakan bai takaita ga shiga wasu kasashen waje domin sayen kungiyoyin wasan kwallo kadai, ko wani otel ko wani club ba, maimakon haka kamata ya yi kamfanonin kasar Sin su gudanar da wasu harkokinsu a ketare. Ta haka ne baya ga ci gaba da kamfanonin na kasar Sin za su samu, za kuma su samar da damar bunkasa ga sauran kasashe ko shiyyoyin da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya wadda kasar Sin ta gabatar. Misali, a fannonin fasahohin zamani, da ayyukan gyara kayayyaki, inda kamfanonin kasar Sin suka fi rinjaye."

Tsohon shugaban kasar Slovenia wanda ya halarci taron Danilo Turk ya bayyana cewa, a baya kasar Sin ta fi mai da hankali kan karuwar GDP, amma yanzu ta fi mai da hankali kan ingancin tattalin arziki, shi ya sa kamata ya yi a kara ba da muhimmanci kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin yin kirkire kirkire, yana ganin cewa, makomar hadin gwiwa a fannin dake tsakanin Sin da tarayyar Turai tana da haske, ya ce, "Muna bukatar karin damammakin samun ci gaba, da cudanyar kimiyya da fasaha, a saboda haka muna fatan sassan biyu wato Sin da tarayyar Turai za su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin kimiyya da fasaha, da kuma manufar zamantakewar al'umma baki daya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China