in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kori shugabannin 'yan sanda da na leken asiri a Somalia
2017-10-30 10:52:20 cri
Ministan labaran kasar Somalia Abdirahman Osman Yarisow, ya tabbatar da korar shugabannin rundunar 'yan sanda da na hukumar leken asiri na kasar, biyo bayan hari na 2 da aka kai birnin Mogadishu da ya yi sanadin rayuka 23, makonni 2 bayan wani harin bam cikin wata babbar mota da ya kashe sama da mutane 300.

Abdirahman Osman Yarisow ya ce a jiya ne majalisar zartarwar kasa ta yanke shawarar korar jami'an da suka hada da Abdullahi Mohamed Ali Sanbalolshe na hukumar liken asiri da kuma Abdihakim Dahir Said, shugaban rundunar 'yan sanda.

Korar na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan jami'an tsaro sun shafe tsawon daren ranar Asabar su na artabu da mayakan Al-shaabab, a kokarin kawo karshen kofar rago da mayakan suka yi wa Otel din Nasa Hablod II na birnin Mogadishu, bayan sun tada bam tare da kutsawa ciki.

Harin ya biyo bayan wanda aka kai ranar 14 ga wannan watan, wanda aka bayyana a matsayin hari mafi muni a tarihin kasar da ya yi sanadin rayuka sama da 350.

A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka nada Abdullahi Sanbalolshe da Abdihakim Dahir, bayan wani tankade da rairaya da shugaban kasar Mohammed Abdullahi Mohammed ya yi ga hukumomin tsaron kasar, kasa da makonni biyu bayan ya kama aiki.

A baya, cikin shekarar 2014, Sanbalolshe ya taba rike mukamin na shugaban hukumar leken asiri na wani dan lokaci kafin daga bisani a tura shi Birtaniya a matsayin jakadan kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China