171027-an-yi-wa-kundin-tsarin-jks-gyaran-fuska-a-yayin-babban-taron-wakilan-jamiyyar-karo-na-19.m4a
|
Masu sharhi sun bayyana cewa, a halin yanzu kasar Sin ta shiga wani sabon zamani na raya kasa, tunanin da shugaba Xi Jinping ya tsara game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki zai yiwa jam'iyyar jagora wajen nacewa da kuma raya tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, kana zai bude wani sabon babi yayin da al'ummun kasar ke kokarin raya kasarsu.
Idan aka kalli tarihin tarukan wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, za a fahimci cewa, kullum ana gyara dokokin jam'iyyar a lokacin da ya dace, misali a yayin babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19 da aka kammala ba da dadewa ba, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai mulki a kasar ta tabbatar da cewa, yanzu haka yanayin da kasar ke ciki ya sauya, tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin ya shiga wani sabon zamani, a saboda haka, daukacin wakilai mahalarta taron suka amince da cewa, za a kara kyautata tsarin jam'iyyar wato za a kara rubuta "tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki" a cikin kundin tsarin jam'iyyar tare da sauran manyan tunanin, domin ba da jagoranci kan aikin gina jam'iyyar a nan gaba.
Kan wannan muhimmin matakin, zaunannen mataimakin darektan ofishin nazarin manufofin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Xiaohui yana ganin cewa, sabon zamani ya kan bullo da sabbin abubuwa, sabbin abubuwa suna bukatar jagorancin sabon tunani, tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki zai daidaita matsalolin da kasar Sin take fuskanta a sabon zamanin, ya ce, "A sabon zamanin da muke ciki, an samu manyan sauye-sauye a yanayin kasar Sin da na duniya, kana kasar Sin tana samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban daban, shi ya sa ake bukatar wani sabon tunanin jagoranci, shi ya sa shugaba Xi ya gabatar da wannan tunani a irin wannan hali, ko shakka babu tunanin zai yiwa jam'iyyar jagora wajen nacewa da kuma raya gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, kana zai bude wani sabon babi yayin da al'umman kasar ke kokarin raya kasarsu."
Tun bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, jam'iyyar ta kara kokari matuka domin raya kasa, misali a matakai daban daban jam'iyyar ta fitar da matakan yin kwaskwarima da yawansu ya zarta 1500 a cikin shekaru biyar da suka gabata, har an samu babban sakamako a kasar, musamman ma a fannin raya tattalin arziki, duk da cewa, tattalin arzikin kasashen duniya yana tafiyar hawainiya, amma tattalin arzikin kasar ta Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata, har ya taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya kamar yadda ake fata. Dalilin da ya sa haka shi ne domin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping ta bullo da "tunanin Xi Jinping game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki" bisa bukatun zamanin.
Wang Xiaohui ya yi nuni da cewa, tunanin yana kunshe da ra'ayoyin kirkire kirkire da dama, hakan zai ba da jagoranci kan aikin raya gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, tare kuma da ciyar da tunanin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin gaba, ya ce, "Babban sakatare Xi Jinping ya amsa tambayoyi a jere game da yadda za a cimma burin raya gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki da ra'ayoyin kirkire kirkire daya bayan daya, hakan zai yi jagoranci kan aikin raya gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, tare kuma da ciyar da tunanin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin gaba."
Jami'in hukumar ladabtarwa ta kwamitin tsakiya ta JKS dake wakilci a ofishin ladabtarwa na kwamitin sa ido kan dukiyar kasa na majalisar gudanarwar kasar Jiang Jinquan yana ganin cewa, nan gaba JKS za ta kara karfafa aikin gudanar da harkokinta bisa doka, ya ce,"Nan gaba jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin gina kanta daga dukkan fannoni, musamman ma a fannin yaki da cin hanci da rashawa, wannan zai sa ta cimma burinta na samun karbuwa da goyon baya daga wajen al'ummun kasar, tare kuma da biyan bukatun sabon zamani."(Jamila)