in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar Sin da na kasashen waje sun bayyana kyakkyawan fatansu ga makomar kasar Sin
2017-10-26 11:09:45 criJiya Laraba ne, a yayin cikakken zaman taro na farko na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da aka yi a birnin Beijing, aka zabi sabbin shugabannin kwamitin koli na jam'iyyar, inda aka sake zabar Xi Jinping a matsayin babban sakatare. Yayin da wadannan sabbin shugabanni ke ganawa da manema labarai, Xi Jinping ya tabbatar da alkibla da za'a bi nan da shekaru biyar masu zuwa, gami da bayyana wasu muhimman ayyukan da jam'iyyar za ta gudanar a nan gaba, al'amuran da suka jawo hankalin al'umma a gida da waje sosai.

Shugaban gidauniyar Kuhn na kasar Amurka, Dokta Robert Lawrance Kuhn, wanda ya jima yana nazarin batutuwan da suka shafi kasar Sin, ya halarci ganawar sabbin shugabannin jam'iyyar Kwaminis da manema labarai. Kuhn ya nuna yabo matuka ga furucin Xi Jinping, kana, ya bayyana kyakkyawan fatansa ga makomar kasar, inda ya ce:

"Jawabin da babban sakatare Xi Jinping ya yi, jawabi ne na hangen nesa, inda ya tabo wasu muhimman abubuwan da aka tattauna a wannan taro, abun da ya sa muka kara fahimtar wasu manyan tsare-tsaren da aka bullo da su a wajen taron. An kuma rubuta wasu manyan manufofi cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar Kwaminis, ciki har da tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, da shawarar 'ziri daya da hanya daya' da sauransu. Wadannan manufofi na da muhimmancin gaske ga kokarin cimma wasu muhimman buri biyu da jam'iyyar Kwaminis ta kafa, wato, na farko, tabbatar da ganin an kafa zaman al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni a yayin da jam'iyyar Kwaminis ta cika shekaru 100 da kafuwa, na biyu kuma shi ne, kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, bin tsarin demokuradiyya, wayin kai da kuma jituwa nan da shekara ta 2049, wato yayin da aka cika shekaru 100 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar ta Sin. Sabbin zaunannun membobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin, shugabanni ne nagari, don haka na yi imanin cewa, kasar Sin za ta kara samun bunkasuwa nan gaba."

Shi ma a nasa bangaren, babban darektan kamfanin zuba jari na kasar Isra'ila, wato Infinity Group, Mista Amir Gal Or cewa yayi, kasar Sin za ta kara taka rawar a-zo-a-gani a harkokin duniya, inda ya ce:

"Mun ga yadda tsoffin shugabannin kasar Sin suka mika mulki ga sabbin shugabanni cikin lumana, al'amarin da ya nuna irin kudirin da aka zartas a yayin babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19. Haka kuma, ina fatan muhimmin tunanin da gwamnatin kasar Sin ta bullo da shi, na raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkanin bil'adama zai samu amincewa a fadin duniya baki daya. Na yi imanin cewa, kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya, da samar da karin alfanu ga dukkan al'umma."

Su kuma al'ummar Sinawa na ganin cewa, jawabin da Xi Jinping ya yi, ya kara musu kwarin-gwiwa game da zaman rayuwarsu a nan gaba. Mista Tao, wanda ke aiki a jami'ar kula da harkokin tsaro ta rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa cewa:

"Babban sakatare Xi ya ce, ya kamata jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta ba da muhimmanci ga batun al'amuran yau da kullum da ya shafi fararen-hula, tare kuma da mayar da kyakkyawan fatan jama'a ga zaman jin dadi a matsayin babban burin da jam'iyyar ke son cimmawa. Babu tantama, furucin Xi ya bayyana ainihin abubuwan da fararen-hula ke tunani a zukatansu, wanda ya ba mu kwarin-gwiwa da kwanciyar hankali. Na yi imanin cewa, a karkashin jam'iyyar Kwaminis wadda Xi Jinping ke jagoranta, kasar Sin za ta kara samun wadata, da arziki, da karfi a duniya, kana, al'ummar kasar za su kara jin dadin zaman rayuwa."

A nata bangaren, wata baiwar Allah dake aiki a harkar zirga-zirgar jiragen kasa a kasar Sin, Song Tingting ta nuna cewa:

"Babban sakatare Xi ya tabo maganar Burin kasar Sin. A ganina, wannan buri buri ne na kowannenmu. A matsayina wadda ke aiki a fannin zirga-zirgar jiragen kasa, kamata ya yi mu yi tsayin daka wajen gudanar da ayyukanmu, da gadar kyawawan abubuwa, tare kuma da ci gaba da raya su. Ya kamata mu dukufa ka'in da na'in kan ayyukanmu, da bada gudummawa domin cimma babban burin kasar Sin."

Har wa yau, akwai Sinawa da dama wadanda suka bayyana kyakkyawan fatansu ga makomar kasa baki daya, ga wasu daga cikinsu:

"Ya kamata mu zage damtse wajen gudanar da ayyukanmu."

"Aikina ya shafi fasahohin sadarwa, ina fatan sana'armu za ta kara samun kyakkyawar makoma."

"Ina fatan rayuwa za ta dace da zamani, ta yadda jama'a za su kara samun saukin zaman rayuwa."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China