in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# Xi Jinping: Kasar Sin za ta kara samun wadata da karfi nan da shekara ta 2019
2017-10-25 13:06:50 cri
Yayin da yake bayani kan manyan ayyukan da za'a gudanar a shekaru biyar masu zuwa, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya ce, shekara ta 2019, shekara ce ta cika shekaru 70 cif da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Kasar za ta kara bin sabon manufar neman bunkasuwa cikin lumana, da habaka tattalin arzikinta ta hanyar da ta dace kuma cikin dogon lokaci, ta yadda daukacin al'ummar kasar Sin da na kasashe daban-daban za su amfana

Har wa yau, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da ayyuka daban-daban karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, da bullo da sabbin shirye-shiryen raya kasa a nan gaba, a wani mataki na bunkasa ayyuka daga fannoni daban-daban. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China