Sakamakon karfafar hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a 'yan shekarun nan, kasar Sin na kara inganta samar da manyan ababen more rayuwar jama'a a kasashen Afirka daban-daban. Amma idan mun dubi tarihi, za mu iya gano cewa, a shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta taba bada tallafin shimfida wani katafaren layin dogo a nahiyar Afirka, wanda ya zama wani abun dake shaida dadadden zumunci da kyakkyawar hulda tsakanin Sin da Afirka. Wannan shi ne, layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya. A cikin shirinmu na wannan mako, za mu kawo muku wani labari, dangane da yadda wannan layin dogo ke kawo kawo moriya ga jama'ar Afirka da kasar Sin.
171031-Kyautata-layin-dogo-tsakanin-Tanzaniya-da-Zambiya-zai-kawo-moriya-ga-Sin-da-Afirka.m4a
|