Taron na yini biyu zai tattauna yadda jama'a za su rika zirga-zirga cikin 'yanci da tsare-tsaren Tarayyar Afrika AU kan kaurar jama'a da kuma matakin da kasashen duniya suka cimma kan batun.
Taron wanda ke zuwa kwanaki 3 bayan wani taron masana kan batun, ya samu halartar ministocin kasashen nahiyar 30 wadanda ke kula da shige da fice.
Wani rahoton Bankin raya nahiyar Afrika ADB ya ce a shekarar 2016, mazauna nahiyar Afrika na bukatar visa kafin shiga kaso 54 cikin dari na sauran kasashen nahiyar. (Fa'iza Mustapha)