in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 sun yi zaman taronsu na biyu
2017-10-20 20:35:21 cri
Yau Jumma'a da yamma ne, shugabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 suka yi zama na biyu a babban dakin taro na jama'a dake birnin Beijing.

Taron wanda shugaba Xi Jinping ya jagoranta, ya amince da daftarin kudurori game da rahoton kwamitin tsakiya na taron wakilan JKS karo na 18, da rahoton aikin kwamitin sa-ido da ladabtarwa da kuma gyaran da ake son yiwa kundin tsarin jam'iyyar, wadanda za'a gabatar da su ga tawagogin wakilan jam'iyyar don su tattauna.

Har wa yau, taron ya amince da sunayen mutanen da za su zama membobin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, da membobi masu jiran kujeru na kwamitin, tare kuma da sunayen mutanen da aka shawarta su zama mambobin kwamitin sa-ido da ladabtarwa, wadanda za a gabatar da su ga tawagogi daban-daban domin su duba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China