Kabilar Dulong na daya daga cikin kabilu 56 na kasar Sin, kuma akasarinsu suna zaune ne a karkarar Dulongjiang ta yankin Nujiang na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar. Sai dai ana daukar lokaci mai tsawo kafin a shiga karkarar tasu, saboda hanya daya ce ta shiga yankin wadda aka gina kan duwatsu. Idan kuma dusar kankanra ta sauka, hanyar ba ta biyu wa, a wani lokaci sai an kai kusan tsawon rabin shekara ba a shiga karkarar ba. A sabili da rashin ci gaban hanyoyi, karkarar Dulongjiang ta dade da kasancewa daya daga cikin sassa masu fama da koma bayan tattalin arziki a lardin Yunnan da ma kasar Sin baki daya. Amma a cikin 'yan shekarun baya, a kokarin da gwamnatin kasar Sin ke yi na saukaka fatara a duk fadin kasar, an magance wannan matsalar, har ma ya kai ga saukaka fatara a wannan yanki.
A biyo mu cikin shirin, domin jin karin bayani.(Lubabatu)
171020-hanyar-da-ta-fitar-da-yan-kabilar-Dulong-daga-kangin-talauci-lubabatu.m4a
|