Yayin da ake gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 19 a kasar Sin, Simon Khaya Moyo, mamban kwamitin siyasa na tsakiya na jam'iyyar Zanu-PF ta kasar Zimbabwe, kuma ministan kula da harkokin watsa labaru na kasar ya ce, cikin shekarun baya, kasar Sin ta taimakawa Zimbabwe wajen gaggauta raya kasa a sassa daban daban, kamar yadda yake kunshe cikin rahoton siyasa da babban sakataren JKS Xi Jinping ya gabatar yayin bude taron.
Khaya Mayo ya ce tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin ya shiga sabon wa'adi, wanda ya nuna cewa, ana raya tsarin a sassa daban daban kasar.
Ya ce wannan na fadada hanyar zamanantar da kasashe masu tasowa, kuma kasashen duniya da ke fatan gaggauta raya kansu, sun samu sabon zabi.
Mista Moyo ya kara da cewa, yanzu Zimbabwe tana koyon yadda Sin take raya kasa, domin kaddamar da aikin kafa yankin musamman na tattalin arziki. (Tasallah Yuan)