in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Afirka sun taya murnar bude babban taron JKS karo na 19
2017-10-20 09:49:26 cri

A yayin da ake gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 19 a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wasu shugabannin kasashen Afirka sun buga waya ko aika da wasika ga kasar Sin domin taya murnar bude taron.

Moussa Faki, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU ya bayyana cikin wasikarsa cewa, JKS ta jagoranci kasar Sin wajen samun nasarar yin gyare-gyare kan tattalin arziki da zaman al'ummar kasar cikin shekaru gomai da suka wuce, tare da ba da babbar gudummowa wajen kara azama kan samun zaman lafiya da tsaro da wadata a duniya. Babban taron wakilan JKS karo na 19 zai sake gwada nagartacciyar kwarewar JKS wajen ba da jagora. AU na saran inganta dankon zumunci a tsakaninta da Sin.

Mataimakin babban sakatare na farko na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu Solly Mapaila, ya bayyana cikin wasikarsa cewa, a karkashin shugabancin babban sakatare Xi Jinping, kasar Sin tana kara azama kan yin kwaskwarima kan tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa cikin adalci. Martabar kasar Sin ta samu ingantuwa, kana tsarin gurguzu ya kara ba da tasiri a duniya. Babban taron wakilan JKS karo na 19 zai tsara manufar raya kasar Sin a nan gaba, kuma zai ba da babban tasiri kan ci gaban duniya.

Har ila yau, a cikin wasikarsa, mista Matthaus, sakataren sashen harkokin waje na jam'iyyar 'yantar da jama'ar kasar Angola ya ce, Angola na fatan an cimma manufar da aka tsara a baya a yayin babban taron, tare da samun cikakkiyar nasara. Tana fatan huldar hadin gwiwa da abokantaka da taimakon juna dake tsakanin jam'iyyun 2 da jama'ar kasashen 2 za ta samu ingantuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China