in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya bukaci 'yan JKS su kaddamar da raya kasar Sin mai tsarin gurguzu ta sabon zamani
2017-10-18 14:08:38 cri

Yau Laraba 18 ga wata ne a nan Beijing aka bude babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, inda babban sakataren jam'iyyar Xi Jinping a rahoton da ya gabatar, ya bukaci dukkan 'yan jam'iyyar da kada su manta da ainihin burinsu na shiga jam'iyyar, da nauyin da aka dora musu, inda ya bukace da su yi namijin kokarin kafa zaman al'umma mai walwala, su kuma fara sabbin ayyukan raya kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani.

A cikin rahoton da ya gabatar a gaban wakilai fiye da 2300, wadanda suka wakilci 'yan jam'iyyar miliyan 89 ko fiye da haka, mista Xi ya ce, ainihin burin 'yan JKS da kuma nauyinsu su ne kawo wa jama'ar Sin alheri da kuma inganta rayuwar da al'ummar Sinawa. Sakamakon kokarin da aka dade ana yi, ya sa, tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin ya shiga sabon zamani, wanda ya zama kashin bayan raya kasar ta Sin.

Mista Xi ya jaddada cewa, nauyin dake kan JKS a sabon zamanin da ake ciki shi ne inganta rayuwar al'ummar Sinawa. Don haka ya zama tilas jam'iyyar JKS da jama'ar Sin su tsaya da kuma ci gaba da kyautata tunanin tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin da muhimman tsare-tsare da aka shata bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, a kokarin samar da al'umma mai walwala nan da shekarar 2020, da tabbatar da zamanintar da tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da kuma kokarin kafa kasar ta Sin ta gurguzu da zamani mai wadata, dimokuradiyya, wayin kai, jituwa, da karfi, nan da shekaru 2050.

A cikin rahoton da ya kaddamar, babban sakataren JKS Xi Jinping ya yi bayani cewa, har kullum 'yan jam'iyyar JKS suna mayar da batun kara ba da gudummawa ga ci gaban dan Adam a matsayin nauyin da ke kansu. Kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar raya kasa cikin lumana, ta kuma yi kira ga jama'ar kasashen duniya da su hada kansu wajen samar da makomar dan Adam mai kyau tare. Har ila yau kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen waje domin raya kanta. Yayin da take daidaita al'amuran kasa da kasa, kasar Sin za ta tattauna da sassa daban daban, a kokarin cin gajiya tare. Za kuma ta ci gaba da sauke nauyin dake kanta a matsayin wata babbar kasa. Sannan za ta shiga a dama da ita cikin aikin yin gyare-gyare kan tsarin daidaita al'amuran duniya, gwargwadon hikimarta da karfinta. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China