Daga watan Satumba zuwa watan Nuwamban shekarar 2017 ne aka gudanar da bikin nune-nunen muhimman cigaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru biyar da suka gabata. Bikin an gudanar da shi ne a wani muhimmin waje da aka tanada a birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Nune-nunen ya shafi irin ci gaban da kasar Sin ta samu ne a fannoni daban-daban da suka hada da ci gaban kimiyya da fasaha, kirkire-kirkire, fasahar masana'antu, fasahar mutun-mutumi, fasahar tauraron dan adam, noma na zamani, kiyaye muhalli, na'urorin kiwon lafiya, kayan aikin soji, na'urorin motsa jiki, da dai sauransu. Alal misali a bangaren tattalin arziki akwai alkaluma da mahukuntan kasar suka fitar na irin nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin wadannan shekaru biyar na karuwar mizanin karfin tattalin arziki na GDP wanda aka yi hasashen samun kashi 6.5 inda ci gaban alkaluman ya karu zuwa kashi 6.9 a watan Yuni shekarar 2017. Sannan kasar Sin ta cimma nasarar fitar da mutane sama da miliyan 43 daga kangin talauci tsakanin shekarar 2012 zuwa shekarar 2016. A fannin kirkire-kirkirkire kuwa, kamfanoni da masana'antun kasar Sin sun samu gagarumin ci gaba ta hanyar amfani da sabbbin fasahohin zamani wanda hakan ya taimaka musu wajen kara adadin kayayyakin da suke samarwa na amfanin cikin gida har ma da wanda ake fitar da su zuwa kasashen duniya. Batun harba tauraron dan adam, cikin shekaru biyar da suka gabata kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan adama a fannoni da dama, da suka hada na hasashen yanayi, ingacin iskar da ake shaka, da gudanar da bincike da tattara bayanan kan teku da tsibbirai da sadarwa da dai sauransu. Batun sufuri an nuna irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kera jiragen kasa masu saurin tafiya don saukakawa al'ummarta a sha'anin zirga-jiraga, kana a ranar 2 ga watan Mayun shekarar 2017 ne, aka kaddamar da jirgin sama samfurin C919 wanda kasar Sin ta kera da kanta. An nuna wasu kayatattun wuraren da kasar Sin ta samar sakamakon ayyukan kiyaye muhalli da dashen itatuwa, lamarin da ke janyo hankalin masu yawon shakatawa a cikin da wajen kasar Sin. Mahalarta taron ya kunshi 'yan jaridu daga sassa daban daban na gidan radiyon kasar Sin da sauran kafafen yada labarai da jaridu na gida da na ketare, da kuma manyan jami'an ofisoshin jakadancin kasashe daban daban dake aikin a kasar Sin. (Ahmad/Ibrahim/Sunusi)
171018-Bikin-nune-nunen-cigaban-da-kasar-Sin-ta-samu-cikin-shekaru-5.m4a
|