in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan Kongo Brazaville: Kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping abin koyi ne gare mu
2017-10-17 10:43:57 cri

A ran 30 ga watan Maris na shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a Jamhuriyar Congo, a yayin ziyarar, shi da takwaransa Denis Sassou N'guesso na Jamhuriyar Congo sun halarci bikin kaddamar da dakin karatu da dakin kasar Sin wanda kasar Sin ta gina a jami'ar Marien Ngouabi, ta kuma bada shi kyauta ga Jamhuriyar Congo, har ma sun ziyarci kwalejin Confucius da aka kafa a dakin kasar Sin. Mr. Bruno Jean Richard Itoua, ministan kula da harkokin jami'o'in Jamhuriyar Congo da ofishinsa ke makwabtaka da dakin kasar Sin a cikin laburaren, yana ganin cewa, kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping a halin yanzu, ta kasance abin koyi ga Jamhuriyar Congo.

Kafin ya hau kan mukaminsa na yanzu, Mr. Itoua shi ne babban direktan kamfanin man fetur na Jamhuriyar Congo, sannan ministan kula da makamashi da albarkatun ruwa, kuma tsohon minista ne mai kula da harkokin nazarin kimiyya da kirkire-kirkiren sabbin fasahohin zamani na kasar. Ya sha kawowa kasar Sin ziyara har sau da dama, har ma ya taba ganawa da shugaba Xi Jinping na kasar Sin. A ganinsa, shugaba Xi da takwaransa Sassou N'guesso sun halarci bikin kaddamar da laburaren jami'ar Marien Ngouabi da kansu lamari ne mai muhimmanci. Mr. Itoua yana ganin cewa, "Dakin karatun ba ma kawai shi ne mafi girma a wannan jami'ar ba, har ma ya kasance dakin karatu mafi girma a duk fadin kasarmu. Abin da ya kamata a ambato shi ne, an kafa kwalejin Confucius a cikin laburaren, shi ne wata alama ce ga laburaren da dakin kasar Sin dake cikin laburaren. Shugaba Xi Jinping ya kaddamar da ziyararsa ta farko a Afirka tun bayan da ya hau kan mukamin shugabancin kasar Sin, Jamhuriyar Congo ta kasance kasar da ya halarci bikin kaddamar da wani laburare a ziyararsa ta farko a kasashen waje, wannan ya alamta cewa, bada ilmi lamari ne mafi muhimmanci ga kasashe masu tasowa, ya kuma alamta cewa, kasar Sin na nunawa Jamhuriyar Congo goyon baya a fannin tarbiya."

Sannan minista Itoua ya nuna yabo sosai ga ci gaban da kasar Sin ke samu a fannonin siyasa da tattalin arziki da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Afirka a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping. Ya kara da cewa, "Kasar Sin tana da tsarin siyasa maras tada hankali, sannan tana da hukumomi wadanda suke aiki kamar yadda ake fata, dukkansu abin koyi ne gare mu. A ganina, abin da ya fi muhimmanci shi ne, shugaba Xi Jinping ya fi mai da hankali kan huldar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Yanzu, bisa dandanlin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, musamman a yayin taron koli na Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu, kasar Sin ta nuna goyo baya matuka ga ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar al'umma a kasashen Afirka. Shugaba Xi ya nuna sahihancinsa kan irin wannan hadin gwiwa. A bayyane take kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ce mafi muhimmanci gare mu a duk duniya. Bisa goyon bayan shugaba Xi, da goyon bayan kasar Sin, muna samun sakamako da dama sabo da mun yi hadin gwiwa da kasar Sin."

Bugu da kari, Mr. Itoua ya nuna cewa, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa ne, shugaba Denis Sassou N'guesso na Jamhuriyar Congo ya taba kawowa kasar Sin ziyara har sau biyu. Yanzu kasashen biyu na kokarin kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban. Mr. Itoua ya jaddada cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta riga ta zama abin koyi ga Jamhuriyar Congo, "A karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta samu sabon ci gaba a fannoni daban daban. Sakamakon haka, ta kafa wani sabon shafi na ci gaba ga Afirka, har ma ga duk duniya baki daya. Ina farin ciki sosai. Kasar Sin abin koyi ne gare mu, ya kamata mu yi koyi da ita domin kokarin cimma burinmu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China