171015-Ba-mu-da-dalilin-rashin-gudanar-da-ayyukanmu-yadda-ya-kamata-a-cewar-Du-Liqun-Bilkisu.m4a
|
Du Liqun, ita ce shugabar ma'aikatan jinya a sashen kula da masu fama da cutar kanjamau na asibitin al'umma na hudu na birnin Nanning dake jihar Guangxi mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Zhuang ta kasar Sin. Wannan jami'a 'yar kabilar Zhuang ta samu babbar nasara a yayin da take gudanar da ayyukanta, wannan ya sa ta samu damar ganawa da shugaban kasar Xi Jinping. Kwanan baya, wakiliyar mu ta kai mata ziyara, inda ta bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya mai da hankali sosai kan harkokin hadin kan al'umma da shawo kan cutar kanjamau, don haka, babu mu da dalili da zai sa mu kasa gudanar da ayyuka yadda ya kamata. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani ne game da wannan ma'aikaciya 'yar kabilar Zhuang mai suna Du Liqun.