in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 40 sun mutu a harin mota da aka kai Mogadishu
2017-10-15 14:08:07 cri
A jiya Asabar 'yan sandan kasar Somaliya sun tabbatar da cewa, mutane a kalla 40 ne suka hallaka a yayin da wasu da dama suka jikkata a sakamakon harin mota da aka kai wani otel da ke birnin Mogadishu. An ce, galibin wadanda suka mutu fararen hula ne, harin ya kuma lalata wasu gine-gine dake daura da otel din.

Ma'aikatan tsaro sun killace wurin, suna kuma gudanar da bincike dangane da harin.

Ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya yi shelar daular alhakin harin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China