in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta cimma burin samun ci gaban tattalin arziki na kimanin kashi 6.5 cikin dari a bana
2017-10-11 13:32:19 cri

Shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin mista Ning Jizhe ya bayyana a birnin Beijing jiya Talata cewa, cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta rika samun saurin karuwar tattalin arziki, kuma tattalin arzikin kasar ya gudana yadda ya kamata, karfin kasar daga dukkan fannoni da ma tasirin da kasar ke bayarwa a duniya suna ta kyautatuwa. Bugu da kari Mr. Ning ya fayyace cewa, babu matsala, kasar Sin za ta iya cimma burin samun bunkasar tattalin arziki na kimanin kashi 6.5 cikin dari a bana.

Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta bayar sun bayyana cewa, matsakaiciyar jimillar GDP da kasar Sin ta samu ta karu da 7.2% daga shekarar 2013 zuwa 2016, wadda ta zarce jimillar da duniya ta samu wato 2.6% da kuma jimillar da kasashe masu tasowa suka samu wato 4%, darajar wannan karuwar tattalin arzikin kasar Sin kuwa ta wuce Yuan biliyan 4400. Shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin mista Ning Jizhe ya bayyana a yayin taron manema labaru na ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin da aka shirya jiya Talata, cewar

"A cikin wadannan shekaru da suka gabata, matsakaiciyar jimillar GDP da kasar Sin ta samu ta karu da kashi 7.2%, jimillar hauhawar fasashin kaya kuwa ta kai kashi 2%, jimillar masara aikin yi a kasar Sin ta kai kiminin kashi 5%. Lallai yadda ake gudanar da harkokin tattalin arzikin kasar Sin yanzu wato yana samun saurin karuwa, da samar da yawan guraban aikin yi, da ma farashin kaya da ya dace yana da kyau sosai, har ma ba a iya samun irinsa a duk fadin duniya."

Alkaluman kididdigar sun nuna cewa, a shekarar 2016, jimillar GDP ya kai Yuan biliyan 74000, wadda ta ninka sau 1.32 bisa ga shekarar 2012. Yawan hatsi da nama da gyada da karfe da motoci da kasar Sin ta samar kuma ya kai na farko a duniya. Tsawon layin dogo mai matukar sauri ma ya kai kilomita dubu 23, wanda shi ma ya zama na farko a duniya. Bugu da kari, ya zuwa karshen watan Satumba na bana, kudin masanya da kasar ta tanada ya kai dala biliyan 3090, wanda shi ma ya zama na farko a duniya.

A ganin Mr. Ning Jizhe, wadannan alkaluman sun nuna cewa, yanzu karfin kasar Sin daga dukkan fannoni yana ta karuwa, haka ma tana ta takawa muhimmiyar rawa a harkokin duniya. Ning ya kara da cewa,

"Jimillar GDP da kasar Sin ta samu a shekarar 2016 ya kai dala biliyan 11200, wadda ta kai kashi 14.8 cikin dari bisa ta duniya. Daga shekarar 2013 zuwa ta 2016 kuwa, yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar ga karuwar tattalin arzikin duniya ya kai kimanin kashi 30 cikin dari, wanda ya zarce yawan gudummawar da kasashen Amurka da Japan da masu amfani da kudin EURO suka bayar gaba daya."

A wadannan shekaru biyar da suka gabata, tsarin tattalin arzikin kasar Sin na samun kyautatuwa. An kashe Yuan biliyan 1570 a shekarar bara wajen nazari da kirkire-kirkire, wanda ya karu da kashi 52.5 cikin dari bisa na shekarar 2012, hakan ya sa kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya wajen zuba yawan kudade a fannin nazari da kirkire-kirkire baya ga kasar Amurka.

Yayin da yake yin hangen nesa kan yanayin tattalin arzikin da kasar Sin ke ciki a shekarar bana, Mr. Ning yana ganin cewa,

"yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 6.9% a farkon rabin shekarar da muke ciki. Kuma bisa alkaluman da muka samu, jimillar ribar da manyan kamfanonin masana'tun kasar Sin suka samu a watan Agusta ta karu da kashi 21.6%, wadda ta sheda kyautatuwar ayyukan gudanar da kamfanonin.

Haka kuma alkaluman hada-hadar kamfanoni ko masana'antu na PMI da hukumar kasar Sin ta bayar a watan Satumba ya kai kashi 52.4%, wadda ta kai wani matsayin koli tun bayan shekarar 2012. Hakan muna iya gano cewa, tushen tattalin arzikin kasar Sin na yanzu na da kyau, don haka babu matsala ko kadan kasar Sin ta cimma burin samun bunkasar tattalin arziki na kimanin kashi 6.5 cikin dari a bana kamar yadda ta tsara a baya. Yanzu tattalin arzikin kasar Sin na samun farfadowa, kila zai samu wani sakamako mai kyau."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China