in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban Sin zai sa kaimi ga ci gaban duniya, in ji farfesan Singapore
2017-10-10 11:20:51 cri

Za a gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a ranar 18 ga wata a nan birnin Beijing, a gabannin ranar, farfesa Zheng Yongnian wanda shi ne shugaban cibiyar nazarin harkokin Asiya ta Gabas ta jami'ar kasar Singapore ya bayyana ra'ayinsa game da sakamakon da kasar Sin ta samu yayin da yake zantawa da manema labarai.

Farfesa Zheng Yongnian yana ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu kasar Sin tana kara himmatuwa domin cimma burinta na samun wadata a fadin kasar, tare kuma da bunkasa tsarin gurguzu na musamman na kasar ta Sin, kana jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta riga ta bullo da cikakken shirinta, inda ya bayyana cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, musamman ma tun bayan da aka kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2012, tattalin arzikin kasar Sin bai samu saurin ci gaba kamar yadda ya kamata ba, har ya ragu daga kaso 6.5 cikin dari zuwa kaso 6.7 cikin dari, to, kada a manta, ba zai yiyu ba saurin ci gaban tattalin arziki ya karu a koda yaushe, abu mai faranta ran mutane shi ne gwamnatin kasar Sin ta yi kokari matuka domin dakile matsalar, a saboda haka saurin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin bai gudana cikin sauri ba, sai dai sannu a hankali yake gudana."

Farfesa Zheng Yongnian ya ce, abu mafi muhimmanci yayin da ake kokarin dakile matsalar raguwar saurin ci gaban tattalin arziki shine a hana shi sauka cikin gaggawa, shi ya sa a bayyane ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai mulki a kasar ta dauki matakai, kuma ta samu sakamako armashi.

Farfasa Zheng ya ce, kasar Sin ta samu hanyar data dace yayin da take kokarin raya kasar, to, ko shirin da kasar Sin ta tsara, da kuma hikimar Sinawa za su iya taimakawa sauran kasashen duniya wajen samun ci gaba? Farfesa Zheng ya bayyana cewa, "Ko shakka babu kusan daukacin al'ummun kasashen duniya sun amince cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya, dalilin da yasa hakan shine, kasar Sin ta riga ta kasance kasa ta biyu mafi saurin ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, kana ta riga ta kasance kasa mafi girma wajen cinikayya a duniya, ana iya cewa, kasar Sin tana bada babbar gudumuwa kan ci gaban duniya."

Farfesa Zheng ya ci gaba da cewa, bai dace ba a yi amfani da shirin kasar Sin kai tsaye yayin da ake kokarin neman samun ci gaba, amma tabbas ne sakamakon da kasar Sin ta samu zai amfanawa sauran kasashen duniya, shi yasa sauran kasashen duniya suna iya koyon fasahohin kasar Sin, inda ya bayyana cewa, "Babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, makasudin tsara shirin kasar Sin ba don kawar da hanyar samun ci gaba ta kasashen yammacin duniya bane, sai dai kasar Sin ta gabatar da wani shiri na daban ne domin samar da dama ga saura domin su yi zabi, ko ya dace, ko bai dace ba, a saboda haka muna kiran shi da sunan shirin kasar Sin. Ko shakka babu kasar Sin ta samu babban sakamako tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarimar tattalin arziki da bude kofa ga kasashen duniya kafin shekaru kusan 40 da suka gabata, ya kamata sauran kasashen duniya su yi nazari kan wannan."

Kana farfesa Zheng Yongnian ya ce, wasu kasashen yamma suna kan kai suka kan hanyar samun ci gaba ta kasar Sin, amma hakika dai hanyar samun ci gaba ta kasar Sin wato fasahohin samun ci gaban da kasar Sin za su taimakawa ci gaban sauran kasashen duniya, inda ya bayyana cewa, "Kasar Sin ba ta tsara shirin raya kasarta ta hanyar yin rufa rufa ba, sai dai ta tsara shirin ne karkashin habakar cudanyar tattalin arzikin duniya, ko habakar cudanyar tattalin arzikin shiyya shiyya, ana iya cewa, kasar Sin ta tsara shirinta ne bisa tushen koyon fasahohin saauran kasashe, a saboda haka shirin raya kasar Sin yana da nasaba da shirin raya kasashen duniya, saboda yanzu haka kasa da kasa suna dogaro da juna."

Kazalika, farfesa Zheng yana ganin cewa, idan sauran kasashen duniya suna son koyon fasahahin raya kasa na kasar Sin, ya dace su yi nazari kan fasahohin kasar Sin da kuma fasahohin sauran kasashen duniya baki daya kafin su yi amfani da su, da haka za su iyar samun wata hanyar da za ta fi dacewa da yanayin da kasashensu ke ciki, a karshe dai za su samu ci gaba yadda ya kamata, haka kuma ana iya cewa, hikimar Sinawa tana ba da gudumawa kan ci gaban bil adama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China