171009-tsoffin-jamian-faransa-suna-mai-da-hankali-kan-babban-taron-jks-dake-tafe.m4a
|
A gabannin ranar da za a kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, wato ranar 18 ga wata, wasu tsoffin manyan jami'an gwamnatin kasar Faransa sun bayyana cewa, suna mai da hankali sosai kan batun, su ma suna fatan huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Faransa za ta kara samun ci gaba yadda ya kamata.
Tsohon firayin ministan kasar Faransa kuma shugaban asusun kirkire-kirkire na kasar Jean-Pierre Raffarin ya taba kai ziyara a kasar Sin a shekarun 1970, kana yana gudanar da aikin cudanyar dake tsakanin Sin da Faransa cikin dogon lokaci, yayin da yake zantawa da manema labarai na kasar Sin, ya bayyana cewa, tun bayan da aka kira babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping ya samu babban sakamako daga duk fannoni a fadin kasar Sin, ba ma kawai sakamakon ya samar da moriya ga al'ummun kasar ta Sin bane, har ma ya amfanawa al'ummun sauran kasashen duniya baki daya. Jean-Pierre Raffarin yana ganin cewa, shugabannin kasar Sin suna da hangen nesa saboda suna son yin hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen duniya domin samun ci gaba tare, yanzu haka kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya, musamman ma wajen harkokin diplomasiyya, inda ya bayyana cewa, "Abu ne mai sauki a iya lura cewa, shugabannin kasar Sin suna himmatuwa kan kwaskwarimar da kasar ke yi, jarorancin da Xi Jinping ke yi a kasar Sin yana da muhimmancin gaske ga kasashen duniya, musamman ma game da manufofin diplomasiyyar da ya tsara. Muna farin cikin ganin goyon bayan da yake nunawa MDD, muna farin cikin sauraron jawaban da ya gabatar a yayin taron UNESCO game da wayewar kai, kana muna farin cikin ganin an gudanar da taron kolin G20 cikin nasara a birnin Hangzhou na kasar Sin, ana iya cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake bisa wuyanta a cikin harkokin duniya."
Jean-Pierre Raffarin yana ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri, hakan zai sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin duniya, kana kasar Sin ita ma ta samu babban sakammko a sauran fannoni, misali wajen diplomasiyya, a saboda haka babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 dake tafe ya jawo hankalin al'ummun kasashen duniya matuka.
Shugaban kwamitin shirya tsarin mulkin kasar Faransa kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar wanda shi ma shugaban babban taron sauyin yanayi na birnin Paris Laurent Fabius yana ganin cewa, babban taron JKS karo na 19 yana da muhimmanci matuka, shi ma yana sa ran cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa a nan gaba, inda ya bayyana cewa, "Muna fatan kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa lami lafiya, ta yadda za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban duniya, muna fatan kasashen Sin da Faransa za su ci gaba da gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu yadda ya kamata, musamman ma wajen kiyaye muhalli da dakile matsalar sauyin yanayi."
Babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa wanda shi ne tsohon jakadan kasar dake wakilci a kasar Sin Maurice Gourdault-Montagne ya gaya mana cewa zai kara mai da hankali kan muhimman manufofin da za a fitar da su a yayin babban taron JKS karo na 19, shi ma ya nuna fatansa cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa kamar yadda ake fata. Yayin da yake takalo magana kan huldar dake tsakanin Sin da Faransa, ya bayyana cewa, ya ji dadi sosai yayin da yake aiki a kasar Sin, a sa'i daya kuma, yana cike da imani cewa, ziyarar aiki karo na farko da shugaban kasar Fasanra Emmanuel Macron zai kai a kasar Sin wadda ake shiryawa za ta ingiza huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa, "Kasar Sin muhimmiyar abokiya ce ga kasar Faransa, ina fatan kasar Sin za ta kara taka rawa a cikin harkokin duniya, ni ma ina fatan kasashen biyu wato Sin da Faransa za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin cimma burin samun zaman lafiya da wadata, ko shakka babu ina cike da imani kan wannan."(Jamila)