Jagoran tawagar kasar Sin a babban taron MDD karo na 72 Wu Haitao, ya ja hankalin kasashen duniya da su sanya batun yaki da fatara a sahun gaba, cikin kudurorin su na ci gaba. Wu Haitao ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata, yayin zaman kwamiti na biyu na mahawara, a wani bangare na taron MDD karo na 72 dake gudana.
Wakilin na Sin, ya ce yaki da talauci na a sahun gaba, a jerin kudurorin ci gaba mai dorewa da aka tsara aiwatarwa nan da shekarar 2030, don haka ya dace a yi tarayya, wajen ganin an cimma nasarar wannan kuduri.
Wakilin na Sin ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci ga kasashen duniya su dauki kwararan matakai domin hakan. A daya hannun ya ce ya dace kwamitin na biyu dake da nauyin tabbatar da hadin gwiwar kasashen duniya a wannan fanni, ya yi namijin kokari wajen ganin an kai ga nasarar kudurorin dake kunshe, cikin ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da 2030.
A cewar Mr. Wu, kudurorin za su tabbatar da an cimma moriyar juna tsakanin kasashen duniya yadda ya kamata.
A wani ci gaban kuma, a dai ranar ta Talata, Mr. Wu ya yi jawabi gaban mambobin kwamiti na 3 na taron MDD karo na 72, inda ya jaddada muhimmnacin baiwa sha'anin bunkasa zamantakewar al'umma muhimmnaci.
Kazalika ya bukaci samar da wani tsari mai nagarta na bai daya, wanda zai wanzar da ci gaba, da kariya ga fannonin inganta zamantakewar al'ummar duniya.