A cikin wani fafen bidiyo da aka wallafa a shafin internet, an ji karar harbe harbe da aka yi da bindigogi masu sarrafa kansu. Rahotanni sun nuna cewa, irin karar makaman da aka ji, abu ne mawuyaci a iya sayar da wadan nan bindigogin a shagon sayar da makamai na Amurka.
Jami'an 'yan sanda kuma sun ce, sama da mutane 20 ne suka mutu, a yayin da wasu sama da 100 suka jikkata a harbe-harben na birnin Las Vegas.