170930-an-yi-bikin-baje-kolin-sakamakon-da-sin-ta-samu-cikin-shekaru-5-da-suka-gabata.m4a
|
A jajibirin ranar babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, an kaddamar da bikin baje kolin sakamakon da aka samu a kasar Sin cikin shekaru biyar da suka gabata, a babban dakin baje kolin kayayyaki na birnin Beijing, inda aka nuna wa masu kallo irin nasarorin da aka samu a fannoni goma da suka hada da siyasa da tattalin arziki da al'adu da zamantakewar al'umma da wayewar kai wajen kiyaye muhalli da diplomasiyya da dai sauransu, tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012.
A ranar 26 ga watan Satumban da muke ciki ne aka kaddamar da wannan bikin baje kolin, inda 'yan kallo da yawan gaske suka shiga babban dakin baje kolin domin kallon kayayyaki da takardu da bidiyo da hotunan da aka shirya game da babban sakamakon da aka samu a fannoni daban daban a kasar Sin, cikin shekaru biyar da suka gabata.
A wurin da aka kebe domin nunawa 'yan kallo sakamakon da aka samu wajen samar da ilmi ga daliban dake lardunan dake fama da talauci na kasar Sin, misali jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kabilar Uygur da lardin Yunnan dake kudancin kasar ta Sin, inda aka samar da taimako gare su ta yanar gizo, dalibar dake karatu a jami'ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta birnin Beijing, Zhang Liqin ta shaida mana cewa, ita kanta ta amfana daga aikin, inda ta bayyana cewa, "Yanzu haka an fara gudanar da aikin ba da ilmi ta yanar gizo, ta haka daliban dake karatu a makarantun karkara ko lardunan dake fama da talauci a fadin kasar Sin suna iya yin karatu ta yanar gizo kamar yadda daliban makarantun manyan birane suke yi, ta wannan hanya, ana iya samun ilmi bisa adalci a kasar."
A wurin da aka kebe domin nunawa 'yan kallo sakamakon da aka samu wajen kula da lafiya, malamin makaranta mai shekaru 78 da ya yi ritaya Bai Xuguang ya ce, yanzu abun da ya fi jan hankalinsa shi ne, manufar da kasar take aiwatarwa kan aikin kula da lafiya, a cikin shekaru biyar da suka gabata, adadin kudin da ya kashe a asibiti ya ragu a kai a kai, inda ya ke cewa, "Babu matsalar karancin kudi idan na je asibiti, gwamnatin kasa ta samar mana inshurar lafiya, mu kan biya kaso 5 cikin dari na kudin jinya kawai, a saboda haka muna jin dadin rayuwa."
Baya ga aikin samar da ilmi da na kula da lafiya, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen kyautata rayuwar al'umma, misali karuwar kudin shiga, da fitar da jama'a daga talauci, da samar da muhalli ga masu fama da talauci da sauransu.
Jami'in kula da rayuwar al'umma na hukumar yi wa tattalin arziki kwaskwarima da samun ci gaba ta kasar Sin, wadda ta shirya wannan bikin baje kolin Gong Zhenzhi ya bayyana cewa, "Misali, wajen aikin ba da ilmi, matsakaicin tsawon lokacin da yaran da suka kai shekaru 15 da haihuwa suka samu ilmi a makaranta ya kai shekaru 9.42, matsayin ba da ilmi na kasar Sin ya riga ya kai matsakacin mataki, inda har ya kai sahun gaba a duniya, adadin kudin shiga na al'ummun kasar shi ma yana karuwa a kai a kai, wato a cikin shekaru biyar da suka gabata, adadin albashin da al'ummun kasar suka samu ya karu da kaso 43.5 cikin dari. A fannin aikin kula da lafiya kuwa, an samu gagarumin ci gaba, matsakacin tsawon rai na al'ummun kasar ya riga ya kai shekaru 76.34."
Kana an dauki matakai a jere kan aikin shari'a domin biyan bukatun al'umma yadda ya kamata.
A cikin mutanen da suka shiga babban dakin baje kolin, an ga wasu 'yan kallon da suka zo daga kasashen ketare, 'dan kasar Canada Luke wanda ya zo kallon bikin ya fada mana cikin harshen Sinnanci cewa, "Na taba karanta littafin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta game da babban burin kasar, ina ganin cewa, irin wannan buri zai kasance burin daukacin al'ummun kasashen duniya, wato zaman lafiya da dadin rayuwa da kuma hadin gwiwa."
Daga fannonin rayuwar al'umma da diplomasiyya zuwa fannonin tattalin arziki da shari'a, ana iya kara fahimtar sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata ta hanyar kallon hutuna da bidiyo da kuma kayayyakin da aka shirya, abun da ya sa masu kallon farin ciki kwarai da gaske. A gaban na'urar rubutun kalmomin 'yan kallo, mutane da yawa sun rubuta kalmomi domin nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin da kuma alfaharinsu kan dimbin nasarorin da kasarsu ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata.(Jamila)