170929-an-kammala-aikin-rajistar-sojojin-sin-da-za-su-gudanar-da-aikin-kiyaye-zaman-lafiya-a-mdd.m4a
|
Jiya ranar 28 ga wata ne, kakakin watsa labarai na ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 22 ga wata, an kammala aikin rajistar sojojin kasar Sin wadanda za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, kana, kasar Sin ta kafa rundunar sojojin kota-kwana domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD a wani mataki na kara daukar nauyin dake bisa wuyanta a harkokin kasa da kasa.
A watan Satumban shekarar 2015 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a yayin taron kolin da aka gudanar kan batun kiyaye zaman lafiya na MDD cewa, kasar Sin za ta shiga sabon tsari game da kafa rundunar sojoji kota-kwana da MDD ta tsara, kuma za ta kafa irin wannan rundunar sojojin da yawansu zai kai 8000 ba tare da bata lokaci ba.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian ya yi mana bayani cewa, ya zuwa ranar 22 ga wannan watan da muke ciki, kasar Sin ta kammala aikin rajistar wadannan sojoji a MDD.
Wu Qian ya kara da cewa, sojojin da aka yi musu rajistar a rundunar kota-kwana ta MDD za su ci gaba da gudanar da aikinsu na yanzu, ya ce, "Rundunar sojojin kasar Sin da aka yiwa rijista a MDD, ta hada da bataliyoyin soja 6, da sassan aikin injiniya guda 3, da kuma sassa masu kula da harkokin sufuri guda 3, da manyan cibiyoyin kula da lafiya guda 2, da sassa masu aikin gadi guda 4, da sassan sojojin kwantar da tarzoma guda 3, da kungiyoyin matuka jiragen sama masu saukar ungulu guda 2, da kungiyoyin jiragen sama masu kula da harkokin sufuri guda 2, da kungiyar jiragen sama marasa matuki guda 1, da kungiyar jiragen ruwan yaki guda 1, gaba daya akwai kungiyoyin sana'a guda 28 a fannoni 10. Za a horas da wadannan sojojin ne bisa ma'aunin MDD, kuma za a tura su wurare daban daban a fadin duniya bisa bukatun MDD."
A yayin taron kolin da aka gudanar kan aikin kiyaye zaman lafiya a shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu kan wannan aiki wadanda suka hada da kiyaye ka'idojin kiyaye zaman lafiya na MDD, da kyautata tsarin kiyaye zaman lafiya, da daga matsayin kwantar da tarzoma, da kara samar da tallafi ga kasashen Afirka, kana ya yi alkawari ga MDD cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga aikinta na kiyaye zaman lafiya, musamman ma a fannoni shida, misali za ta kara tura sojojin aikin injiniya da sufuri da likitanci domin su shiga aikin kiyaye zaman lafiya, kana kasar Sin za ta samar da tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 100 ga kungiyar tarayyar Afirka AU domin ta kafa rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da sojojin kwantar da tarzoma, ta yadda za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen nahiyar Afirka yadda ya kamata.
Wu Qian ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da ayyukan lami lafiya, inda yana mai cewa, "Yanzu, kasar Sin ta kammala aikin rajistar wadannan sojoji 8000 a MDD, nan gaba za ta kara horas da su ta yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kana kasar Sin ta kafa rundunar 'yan sanda domin samar da kwanciyar hankali, ban da haka kuma tana shirin samar da taimako ga sauran kasashen duniya wajen horas da sojojin kiyaye zaman lafiya da kuma kwance nakiyoyin da aka binne a baya, kazalika, kasar Sin za ta tura wasu sojojin aikin injiniya da sufuri da likitanci domin su shiga aikin kiyaye zaman lafiya, kana kasar Sin za ta samar da tallafin kudi ba tare da gindaya wani sharadi ba ga kungiyar tarayyar Afirka AU domin ta gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka, yanzu haka tana yin shawarwari da MDD domin kafa asusun shimfida zaman lafiya da samun ci gaba na MDD."
Wu Qian ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta kafa rundunar sojojin kota-kwana na MDD domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da nufin kara daukar nauyin dake bisa wuyanta a harkokin kasa da kasa, ko shakka babu kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa kan aikin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hanlali a shiyya-shiyya, ya ce, "Kasar Sin tana kokari matuka domin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya, kana tana goyon bayan aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, gaba daya kasar Sin ta tura sojojin da yawansu ya kai dubu 36 zuwa wurare daban daban a fadin duniya domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya, abun bakin ciki shi ne 13 daga cikinsu sun rasa rayukansu yayin da suke gudanar da wannan aiki, ana iya cewa, kasar Sin tana taka muhmmiyar rawa kan aikin kiyaye zaman lafiya na MDD."(Jamila)