in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawan yanayin kasuwanci da ake ciki a yankin cinikayya cikin 'yanci ya amfana wa kamfanin GE
2017-09-28 11:01:51 cri

A cikin shekaru 5 da suka gabata bayan da aka rufe babban taron wakilan JKS karo na 18, kasar Sin ta kara bude kofarta ga sauran kasashen duniya, musamman ta amincewa da shigar da jarin waje a bangaren sana'o'in ba da hidima da kirkire-kirkire, baya ga matakan kyautata yanayin tattalin arziki da cinikayya da kasar ta fito da su. Kamfanin GE na daya daga cikin manyan kamfanonin jarin waje wadanda suke tafiyar da harkokinsu a kasar Sin, kamar yadda sauran kamfanoni masu jarin waje suke gamsuwa da sauye-sauyen da aka samu a kasuwar kasar Sin, kamfanin GE ma yana cin gajiyar sabbin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka.

Kamfanin GE, babban kamfani ne dake kan gaba wajen samar da kayayyakin zirga-zirgar sararin sama, da na'urorin wutar lantarki da samar da makamashin da ake sabuntawa da kuma na'urorin kiwon lafiya a duk fadin duniya. A 'yan shekarun nan, a lokacin da kasar Sin take kara bude kofarta ga sauran kasashen duniya, kamfanin GE ma ya samu bunkasuwa cikin sauri.

A watan Satumban shekarar 2014 ne, kamfanin GE ya bude cibiyar tafiyar da harkokinsa a birnin Shanghai ne, wadda za ta rika kula da kasashe da yankuna 17 dake yankin Asiya da tekun Pasifik. Madam Duan Xiaoying, babbar mataimakiyar shugaban kamfanin GE, kuma babbar direkta, kana shugabar sashen GE mai kula da yankin kasar Sin ta gaya wa wakilinmu cewa, an kafa wannan cibiya kuma tana tafiyar da ita cikin nasara sakamakon goyon bayan manufofin da yankin cinikayya cikin 'yanci na Shanghai da aka kafa shi shekara 1 kawai. Madam Duan tana mai cewa, "Cibiyarmu tana ba da hidima ga kasashe da yankuna 17 wadanda suke yankin Asiya da tekun Pasifik. Saboda haka, ana bukatar amfani da harsuna 13, muna bukatar samari wadanda suka kware a wannan aiki, kuma suka fito daga kasashe da yankuna daban daban a cibiyarmu. Manufofin da yankin cinikayayya cikin 'yanci na Shanghai ya tsara sun taimaka mana wajen shigar da su, har ma su iya zama a nan Shanghai ba tare da tashin hankali ba."

A watan Satumban shekarar 2013 ne aka kafa yankin yin cinikayya cikin 'yanci na Shanghai. A cikin shekaru 4 da suka gabata, yankin ya amince da baki 'yan kasuwa su zuba jarin waje a sana'o'in da yawansu ya kai wajen kashi 90 cikin dari bisa na dukkan sana'o'in tattalin arzikin kasar Sin kamar yadda mu Sinawa ke yi. Har ma yawan kamfanoni masu jarin waje da aka kafa a cikin yankin ba tare da bukatar samun amincewa daga wajen hukumomin gwamnati ba ya kai kashi 90 cikin dari. Suna bukatar su sanar da hukuma ce kawai. A takaice dai, a yankin yin cinikayya cikin 'yanci na Shanghai, kamfanoni masu jarin waje, ciki har da kamfanin GE suna cin gajiyar sabbin manufofin da suka shafi harkokin kasuwanci da kwastan da nazarin ingancin kayayyaki da dai sauransu. Irin wadannan sabbin manufofi sun burge madam Duan Xiaoying, mataimakiyar shugaban kamfanin GE, tana mai cewa,"A ganina, suna da bambanci da tsoffin manufofi. Ana kokarin saukaka da hanzarta matakan yin rajista. Idan an gamu da matsala, to, akwai mutumin da zai taimake ka domin magance wannan matsala cikin lokaci. Sakamakon haka, an kammala ajandar kafa cibiyarmu cikin wasu watanni kawai."

Ya zuwa yanzu, birnin Shanghai na kasar Sin ya zama daya daga cikin cibiyoyin nazari da kamfanin GE ya kafa a duk fadin duniya, har ma ya kasance daya daga cikin cibiyoyin tafiyar da harkokinsa guda 3 da kamfanin GE ya kafa a yankin Asiya da tekun Pasifik. Bugu da kari, birnin Shanghai shi ne wurin farko da kamfanin GE ya kafa sashensa na kirkiro sabbin kayayyakin zamani a duk fadin duniya.

Madam Duan Xiaoying ta bayyana cewa, a yayin da kasar Sin take kokarin karfafa yin gyare-gyare, kasar Sin tana kyautata yanayin tattalin arziki da cinikayya a kai a kai domin kokarin jawo karin jarin waje. A lokacin da kasar Sin take hanzarta aiwatar da manufar "kayayyaki kirar kasar Sin nan da shekarar 2025" da shawarar "ziri daya da hanya daya" da kuma shirin "yanar gizo+", Madam Duan ta ce, kamfanin GE yana cike da imani ga makomar kasar Sin, "A ganin kamfanin GE, kasar Sin za ta zama kasuwa mafi girma a duk fadin duniya a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa da wutar lantarki da makamashin da ake sabuntawa da kayayyakin kiwon lafiya da na zirga-zirgar sararin sama da dai makamatansu. Tana da makoma mai haske sosai. Kamfanin GE ba ma kawai yana gamsuwa da makomar kasuwar kasar Sin ba, har ma zai ci gaba da cika alkawuransa na zuba jari a kasar Sin cikin dogon lokaci mai zuwa." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China