A kwanakin baya ne aka shirya taron hadin gwiwar raya masana'antu, tsakanin wasu kasashen Afirka da suka hada da Algeria, da Najeriya, da Sudan ta kudu da Lesotho, da gwamnatin lardin Hunan dake kasar Sin. An gudanar da wannan taro ne tsakanin ranakun Alhamis 21 zuwa Asabar 24 ga watan Satumba.
A yayin taron, tawagar gwamnatin jihar Kano wadda gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta, ta saurara, tare da ganewa idonta irin damammaki dake akwai, a fannin hadin gwiwar raya sassan masana'antu daban daban, ciki har da na ayyukan gona, da samar da ababen more rayuwa, da na hakar ma'adanai da kuma samar da makamashi.
Kaza lika tawagar ta jihar Kano ta gana da wasu wakilan masana'antun samar da irin shuka mai inganci, da na sarrafa na'urori, da motocin aikin noma. Har ila yau ta ziyarci lardin Shandong, inda ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar gina wani yankin masana'antun sarrafa tufafi a jihar ta Kano tare da rukunin kamfanin Ruyi, aikin da zai lashe kudi har dalar Amurka miliyan 600. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)
171004-Taron-hadin-gwiwar-raya-masanaantu-tsakanin-kasashen-Afirka-da-lardin-Hunan-na-kasar-Sin.m4a
|