171003-Zantawar-wakilin-sashin-Hausa-na-CRI-da-gwamnan-jihar-Kano.m4a
|
A yayin taron dai wakilai daga kasashen Najeriya, da Algeria, da Sudan ta Kudu da Losotho, sun saurari irin damammaki dake akwai na hadin gwiwar raya sassan masana'antu daban daban, ciki hadda na ayyukan gona, da samar da abababen more rayuwa, da na hakar ma'adanai da kuma samar da makamashi.
A bangaren Jihar Kano dake arewacin Najeriya, gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar wasu jami'an gwamnatin sa, zuwa lardin na Hunan, inda suka saurari tanaje tanajen dake akwai na hadin gwiwa, sun kuma gana da wasu wakilan masana'antun samar da irin shuka mai inganci, da na sarrafa na'urori, da motocin aikin noma. Kaza lika tawagar ta jihar Kano ta isa lardin Shandong, inda ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar gina wani yankin manasan'antun sarrafa tufafi a jihar ta Kano tare da kamfanin Ruyi Group.
Yayin da gwamnan na jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ke lardin Hunan, wakilin mu Saminu Alhassan ya samu zantawa da shi, inda ya fara da tambayar sa dalilin da ya sanya su ganin dacewar halartar taron na wannan karo.