in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya halarci bikin bude taron kungiyar 'yan sandan kasa da kasa
2017-09-27 10:46:13 cri

Jiya Talata ne, aka kaddamar da babban taron shekara shekara na kungiyar 'yan sandan kasa da kasa a nan birnin Beijing. A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga sassa daban daban da suka halarci taron da su kara hada kai domin samar da makoma ta bai daya mai cike da kwanciyar hankali ga rayuwar bil adam, kana ya gabatar da shawarwari guda hudu kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin tabbatar da shari'a.

Kungiyar 'yan sandan kasa da kasa babbar kungiya ce dake gudanar da hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin kasashen duniya, ko shakka babu tana taka muhimmiyar rawa a aikin zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin 'yan sanda a fadin duniya domin dakile ayyukan ta'addanci da fataucin miyagun kwayoyi da fasa kwaurin da ake aikakatawa, a saboda haka masu aikin shari'a da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa da suka zo daga kasashe 158 ne suka halarci babban taron da aka kaddamar a jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin bikin bude taron, ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna fuskantar kalubale iri iri, misali ayyukan ta'addanci da laifuffukan da ake aikatawa ta yanar gizo da laifuffuka da ake aikatawa a kasahen ketare, inda ya bayyana cewa, "Kasashen duniya suna fuskantar kalubalen tsaro iri guda, shi ya sa batun tsaro muhimmin al'amari ne dake shafar makomar bil adam, idan ana son tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, to ya zama wajibi a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, in ba haka ba, ba zai yiyu a cimma wannan buri ba. Kasar Sin tana son hada kai tare da sauran gwamnatocin kasashen duniya da kuma kungiyoyin kasa da kasa domin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a harkokin 'yan sanda, ta yadda za a samar da makomar bil adam guda daya mai kwanciyar hankali."

Kana shugaba Xi ya gabatar da ra'ayinsa kan aikin hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa wajen tabbatar da tsaron shari'a a fannoni hudu, inda ya jaddada cewa, ya kamata a gudanar da hadin gwiwa ta hanyar yin kwaskwarima da kirkire-kirkire bisa ka'ida, ta haka za a samu moriya tare, ban da haka shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata kasashen duniya su kara mai da hankali kan aikin tsaro da tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa domin samar da cikakken tsaro ga daukacin al'ummun fadin duniya. Kazalika, shugaba Xi ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a nace da kuma kiyaye ka'idojin MDD da na kungiyar 'yan sandan kasa da kasa, tare kuma da aiwatar da yarjejeniyar dakile laifuffukan da ake aikatawa a ketare da yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, saboda ta haka ne za a iya tabbatar da adalci tsakanin al'umma. Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, dole ne manyan kasashe masu ci gaba a duniya su kara nuna goyon baya ga kasashen dake fama da talauci domin samar da tsaro da wadata ga al'ummunsu.

Kana shugaba Xi ya yi bayani cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin kasar Sin tana kokari matuka domin gudanar da harkokin kasa bisa doka cikin kwanciyar hankali, inda yana mai cewa, "Makasudin kokarin gwamnatin kasar Sin shi ne samar da wani muhallin rayuwa mai kwanciyar hankali, ana iya cewa, al'ummun kasar Sin suna jin dadin zaman jituwa, shi ya sa kasar Sin take taka rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a fadin duniya."

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta kara goyon bayan da take baiwa kungiyar 'yan sandan kasa da kasa, da kuma taimaka wa kungiyar wajen gudanar da aikace-aikace cikin hadin gwiwa sau uku a ko wace shekara a fannonin yaki da ta'addanci da kuma yaki da masu aikata laifuffuka ta yanar gizo da dai sauransu. Ban da haka kuma, za ta taimaka wajen inganta kwarewar kungiyar wajen gudanar da ayyukanta bisa dokoki yadda ya kamata, ta yadda za a karfafa tasirin kungiyar a duk fadin duniya.

A karshe, shugaba Xi ya bayyana cewa, "Makomar bil adam tana da haske, amma ba zai yiyu ba a tabbatar da makomar cikin sauki, tilas sai al'ummun kasashen duniya sun hada kai tare, ko shakka babu za a gamu da matsala yayin da ake kokarin tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba, kasar Sin tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya domin cimma burin shimfida zaman lafiya da wadata a fadin duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China